Kashim Shettima Ya Bayyana Yadda Cire Tallafi Zai Kare Lafiyar 'Yan Najeriya, Ya Fadi Amfanin Hakan

Kashim Shettima Ya Bayyana Yadda Cire Tallafi Zai Kare Lafiyar 'Yan Najeriya, Ya Fadi Amfanin Hakan

  • Mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima ya ce daga cikin amfanin cire tallafin man fetur akwai kare lafiyar al'umma
  • Kashim ya bayyana haka ne a taron karawa juna sani na Hukumar Sauyin Yanayi ta Kasa (NCCC) a Abuja
  • Ya ce cire tallafin zai kare 'yan Najeriya daga shakar gurbatacciyar iska saboda raguwar yawan ababan hawa da kuma amfani da man fetur

FCT, Abuja - Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya bayyana amfanin cire tallafi ga lafiyar 'yan Najeriya.

Ya ce cire tallafin zai kare mutane daga shakar gurbatacciyar iska da ta kai Tan miliyan 15 a shekara daya.

Kashim ya bayyana amfani cire tallafi wurin kare lafiyar al'umma
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima Ya Yabi Cire Tallafi Wurin Kare Lafiyar 'Yan Najeriya. Hoto: Daily Trust.
Asali: UGC

Kashim ya yabi karfin halin Tinubu na cire tallafi

Shettima ya bayyana haka ne a taron karawa juna sani da Hukumar Sauyin Yanayi ta Kasa (NCCC) ta gudanar a Abuja, New Telegraph ta tattaro.

Kara karanta wannan

"Shugaba Tinubu Ya Fi Sauran Shugabannin Najeriya", Cewar Jigon APC, Ya Bayyana Kwakkwaran Dalili

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mataimakin shugaban kasar wanda ya samu wakilcin mataimakin shugaban ma'aikatansa, Sanata Ibrahim Hassan ya ce Najeriya na kan turba don ba da gudunmawa ta fannin sauyin yanayi, cewar Thisday.

Ya ce:

"A farkon wannan gwamnatin, Shugaba Tinubu ya yi ta maza ya cire tallafin man fetur a kasar.
" A binciken da hukumar sauyin yanayi ta kasa ta fitar kan amfanin cire tallafin man fetur ya nuna an samu raguwar siyan man da kashi 30.

Kashim ya fadi amfanin cire tallafin ga lafiyar al'umma

Ya kara da cewa kamar yadda Punch ta tattaro:

"Hakan ya kawo raguwar shakar gurbatacciyar iska da mutane ke shaka a kullum har Tan 42,800.
Ya ce hakan bai rasa nasaba da rashin yawan ababan hawa a kan tituna ya assasa saboda raguwar hada-hada a kan hanyoyi.

Kara karanta wannan

Sauƙi Ya Zo: Fadar Shugaban Ƙasa Ta Bayyana Mafi Karancin Albashin da Zata Ƙara Wa Ma'aikata a Najeriya

"Idan aka kwatanta amfanin hakan a shekara, cire tallafin zai kare mutane daga shakar iska gurbatacciya har Tan miliyan 15."

Cire Tallafi: FG Ta Koka Kan Yadda Yawan Shan Mai A Najeriya Ya Ragu Da Lita 18.5m

A wani labarin, Gwamnatin Tarayya ta koka kan yadda 'yan Najeriya suka rage yawan shan man fetur a kasar.

Kamfanin man fetur a kasar, NNPCL ne ya bayyana haka a ranar Lahadi 9 ga watan Yuli a Abuja, kamar yadda rahotanni su ka tabbatar.

Ya ce tsakanin watan Janairu zuwa Mayu na wannan shekara, yawan man fetur da 'yan Najeriya suka sha ya tasamma lita biliyan 9.9.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel