Sojojin Jamhuriyar Nijar Sun Nada Sabon Fira Minista A Kasar Bayan Bijirewa Kungiyar ECOWAS
- Sojin Jamhuriyar Nijar sun nada Ali Mahaman Lamine a matsayin sabon Fira Ministan kasar
- Kakakin gwamnatin kasar shi ya bayyana haka a jiya Litinin 7 ga watan Agusta da dare a fadar shugaban kasa
- Wannan na zuwa ne bayan kungiyar ECOWAS ta ba wa sojin kwanaki bakwai da su mika mulki ga Bazoum
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Yamai, Nijar - Sojojin juyin mulki a Jamhuriyar Nijar sun nada Ali Mahaman Lamine sabon Fira Minista a kasar.
Ali Mahaman tsohon ma'aikacin Bankin Raya Afrika (AfDB) ne kuma tsohon ministan kudi a gwamnatin Mamadou Tandja da aka yi wa juyin mulki a 2010.
Kakakin gwamnatin Jamhuriyar Nijar shi ya sanar da haka a jiya Litinin 7 ga watan Agusta da dare inda ya ce Lamine tsohon ma'aikacin AfDB ne da ke aiki a kasar Chadi.
Sojin Nijar sun kifar da gwamnatin Bazoum
Sojijin sun yi juyin mulki ne a ranar 26 ga watan Yuli inda su ka zargi Mohamed Bazoum da cin hanci da rashin shugabanci mai inganci ga al'ummar Nijar miliyan 26, cewar The Sun Daily.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A gwamnatin Bazoum, kasar ta yi kawance da Faransa da Italiya da Amurka wurin yaki da masu ikirarin jihadi a yankunan Sahel, Aminiya ta tattaro.
Kungiyar Raya Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) ta yi ganawar gaggawa kan juyin mulkin inda ta ba wa sojojin wa'adin kwanaki bakwai da su mika mulki ga Bazoum ko su fuskanci takunkumi.
Sojin Nijar sun yi fatali da gargadin ECOWAS
Takunkumin sun hada da yanke alakar kasuwanci da kudade tsakanin kasashen da daukar matakin soji a kan kasar idan ba su mika mulki ba.
Juyin mulki: Sultan, Fastoci Sun Bayyana Matsayarsu Kan Tura Soji Nijar Da ECOWAS Ke Shirin Yi, Sun Gargadi Tinubu
Sojin kasar sun yi fatali da wannan barazana inda su ka gargadi kungiyar kan shirinta na daukar matakin karfin soji.
A ranar Lahadi 6 ga watan Agusta ne wa'adin ECOWAS na kwanaki bakwai ya kare.
Har ila yau, dakarun Mali da Burkina Faso sun dira a Jamhuriyar Nijar don taimakawa sojin kasar kamar yadda rahotanni suka tabbatar.
ECOWAS: Dakarun Mali Da Burkina Faso Sun Isa Nijar, Bayanai Sun Fito
A wani labarin, dakarun kasashen Mali da Burkina Faso sun dira a Nijar don taimakon kasar kan matsalar da ta ke ciki bayan ECOWAS sun yi barazana ga kasar.
Rahotanni sun tabbatar da ganin dakarun Mali a kasar kamar yadda Hukumar Yada Labarai da Hulda da Jama'a ta Kasar (DIPR) ta wallafa.
Asali: Legit.ng