"Na Fusata Ne Kuma Ga Yunwa": Yadda Wani Bakano Ya Raunata Dan Mai Koko Saboda Ta Ki Siyar Masa Da Bashi

"Na Fusata Ne Kuma Ga Yunwa": Yadda Wani Bakano Ya Raunata Dan Mai Koko Saboda Ta Ki Siyar Masa Da Bashi

  • Alkalin kotun shari'a ta jihar Kano ya jefa wani mutum mai suna Jaafar Lukman a magarkama
  • Mutumin ya raunata dan wata mai koko da kosai saboda ta ki siyar masa da bashi sannan ya tuntsurar mata da kayan sana'arta
  • Lukman ya ce ya fusata ne sannan ga yunwa na nukurkusarsa shiyasa ya yi wa Jamila Mai-Kosai aika-aika

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Kano - Wata kotun shari'a ta jihar Kano da ke zama a karamar hukumar Kiru ta garkame wani mutum, Jaafar Lukman, a gidan gyara hali kan zargin raunata dan Jamila Mai-Kosai, wacce ta ki siyar masa da koko bashi.

An kuma yi zargin cewa ya zubarwa matar da kosai, kullun kosai da kokon da take siyarwa a wata mararraba da ke garin Kano, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Kadu Yayin da Ta Isa Wajen Bikin Mijinta, Aminiyarta Ce Amaryar Da Ya Yi

Alkali ya daure Lukman a gidan gyara hali
"Na Fusata Ne Kuma Ga Yunwa": Yadda Wani Bakano Ya Raunata Dan Mai Koko Saboda Ta Ki Siyar Masa Da Bashi Hoto: Thisday
Asali: UGC

Rundunar yan sandan jihar ta yi zargin cewa wanda ake karar ya je wajen matar da niyan siyan koko da kosai bashi, amma sai ta hana masa saboda tana binsa wasu kudade.

An tattaro cewa bayan ta ki siyar masa da bashin, sai Lukman ya yi amfani da kafarsa wajen tuntsurar da kokon, kosai, kullun kosai da kuma man da take tuya da shi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Dalilin da yasa na tuntsurar da kokon da ji wa yaro rauni, wanda ake kara

Da aka karanto masa tuhumar da ake masa, wanda ake karar ya amsa laifinsa, amma ya fada ma kotun cewa ya fusata ne kuma yana jin yunwa lokacin da ya aikata laifin.

Mai shari'a na kotun, Malam Usman Haruna Usman, ya yi umurnin garkame Lukman a gidan yari sannan ya dage sauraron shari'ar har zuwa ranar 4 ga watan Satumba.

Kara karanta wannan

Matashi Ya Shiga Tasku Bayan Kashe Makwabcinsa Da Ke Shirin Zama Ango, Kotu Ta Yanke Masa Hukuncin Kisa

Yan bindiga sun yi garkuwa da basaraken Nasarawa da kuma matarsa

A wani labari na daban, mun ji cewa wasu tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da basaraken garin Gurku da ke karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa, Jibril Mamman Waziri, da matarsa, Hajiya Sa’adatu Waziri.

Kamar yadda wata majiya ta bayyana, mummunan al'amarin ya afku ne da misalin karfe 10 na dare lokacin da mazauna yankin da dama suka kwanta bacci a gidajensu domin samun hutu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng