Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Basaraken Arewa Da Matarsa

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Basaraken Arewa Da Matarsa

  • Yan bindiga dauke da muggan makamai sun yi awon gaba da basaraken garin Gurku a karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa
  • Mahara sun sace Jibril Mamman Waziri da matarsa, Sa’adatu Waziri a daren ranar Lahadi, 6 ga watan Agusta
  • Rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da yin awon gaba da mutanen zuwa wani wuri da ba a sani ba

Jihar Nasarawa - Tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da basaraken garin Gurku da ke karamar hukumar Karu ta jihar Nasarawa, Jibril Mamman Waziri, da matarsa, Hajiya Sa’adatu Waziri.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa al'amarin ya afku ne da misalin karfe 10 na dare lokacin da mazauna yankin da dama suka kwanta bacci domin samun hutu.

Jami'an yan sanda
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa Da Basaraken Arewa Da Matarsa Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Jaridar Vanguard ta nakalto waata majiya na cewa:

"Da misalin karfe 10 na dare ne lokacin da mummunan al'amarin ya afku. Yan bindigar wadanda suka zo da yawansu sun sace basaraken da matarsa. Basu samu kowani agaji daga hukumomin tsaro ba shiyasa yan bindigan suka yi awon gaba da su.

Kara karanta wannan

Abin Da Ya Jawowa El-Rufai, Danladi Da Okotete Samun Tasgaro a Zama Ministoci

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Muna kira ga yan sanda da sauran hukumomin tsaro da su gaggauta shiga lamarin domin su samu yanci ba tare da bata lokaci ba."

Rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta yi martani a kan sace basarake da matarsa

Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya tabbatar da lamarin a ranar Litinin, 7 ga watan Agusta. Ya ce:

"Ina mai son tabbatar da cewar da misalin karfe 10 na daren ranar 6 ga watan Agusta, rundunar yan sandan jihar Nasarawa ta samu kira mai cike da damuwa cewa yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun farmaki basaraken Gurku, da ke kimanin kilomita 10 daga ainahin garin Mararaba.
"Da samun labari, kwamishinan yan sanda, CP Maiyaki Baba, yatura tawagar hadin gwiwa na yan sanda da kungiyoyin yan banga zuwa wajen da abun ya faru.

Kara karanta wannan

Masu Garkuwa Sun Afkawa Fadar Sarki, Sun Sace Shi Tare Da Mai Dakinsa A Jihar Arewa, 'Yan Sanda Sun Dauki Mataki

"Da isarsu wajen, an gano cewa an yi garkuwa da basaraken da matarsa zuwa wani wuri da ba a sani ba. An kakkabe dukkanin jeji da tsaunukan da ke kewaye amma duk kokarin ceto su ya ci tura.
"Kwamishinan yan sandan ya tura karin jami'ai na rundunar da ke yaki da masu garkuwa da mutane da jami’an rundunar ‘yan sandan yankin Karu zuwa wurin da lamarin ya faru domin ceto basaraken da matarsa ba tare da rauni ba."

Madugun yan daba da ake nema ruwa a jallo a Kano ya mika wuya

A wani labari na daban, mun ji cewa kasurgumin dan daba da ‘yan sanda ke nema ruwa a jallo a Kano mai suna Nasiru Abdullahi da aka fi sani da Chile Mai Doki ya mika wuya ga hukumar.

A makon da ya gabata ne rundunar 'yan sanda a jihar ta sanar da sunayen ‘yan daba uku da take nema ruwa a jallo tare da ba da kyautar N300,000 ga duk wanda ya kawo su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng