WAEC Ta Saki Sakamakon Jarabawar 2023 WASSCE, Ta Bayar Da Sabon Umarni Ga Dalibai

WAEC Ta Saki Sakamakon Jarabawar 2023 WASSCE, Ta Bayar Da Sabon Umarni Ga Dalibai

  • Hukumar shirya jarabawar kammala sakandire a Yammacin Afirika (WAEC) ta saki sakamakon jarabawar ɗaliban da suka zana jarabawar WASSCE ta bana
  • WAEC ta hannun shugabanta a Najeriya, Patrick Areghan, ya tabbatar da sakin sakamakon jarabawar sama da da ɗalibai miliyan 1.6
  • A sakamakon jarabawar na bana an samu ci gaba wajen samun sakamako mai kyau da ɗaliban da suka zana jarabawar suka samu

Yaba, jihar Legas - Hukumar shirya jarabawar kammala karatun sakandire ta West African Examinations Council (WAEC) ta bayyana sakin sakamakon jarabawar West African Senior School Certificate Examination (WASSCE) na shekarar 2023.

Hukumar shirya jarabawar ta kuma bayyana cewa ɗaliban da suka zauna jarabawar za su iya karɓar takardar shaidar zana jarabawar.

WAEC ta saki sakamakon jarabawar 2023
Sakamakon jarabawar WASSCE 2023 ya fito Hoto: The West African Examinations Council, WAEC - Nigeria
Asali: Facebook

WAEC 2023, an samu ci gaba

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa WAEC ta bayyana hakan ne ta hannun kakakinta Patrick Areghan, a ɗakin ganawa da manema labarai na ofishin hukumar na Najeriya dake Yaba a jihar Legas, ranar Litinin 7 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Maryam Shetty: ‘Yan Siyasa, ‘Yan Takara Da Mutane 5 Da Suka Ga Samu Da Rashi

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Hukumar shirya jarabawar ta bayyana cewa daga cikin ɗalibai 1,613,733 da suka zauna jarabawar, an riƙe sakamakon ɗalibai 262,803 bisa rahotannin satar jarabawa, rahoton Premium Times ya tabbatar.

Haka kuma, Areghan ya sanar da cewa an samu ci gaba kan ɗaliban da suka samu nasara a wannan karon, inda jimillar ɗalibai 1,361,608 wanda ke wakiltar kaso 84.38%, suka samu kiredit biyar tare ko ba tare da turanci ko lissafi ba a jarabawar.

Haka kuma ɗalibai 1,287,920 wanda ke wakiltar kaso 79.81% suka samu kiredit ko fiye da haka a aƙalla darussa biyar ciki har da turanci da lissafi.

A kalamansa:

"Ina farin cikin sanar da cewa ɗaliban da suka zauna jarabawar 2023 WASSCE kuma ba su da wata matsala, za su iya duba sakamakon su ciki har da takardar shaidar zana jarabawar."

Kara karanta wannan

"Shugaba Tinubu Ya Fi Sauran Shugabannin Najeriya", Cewar Jigon APC, Ya Bayyana Kwakkwaran Dalili

Legit.ng ta rahoto cewa sakin sakamakon jarabawar da aka yi a ranar Litinin, zai ƙara ƙarfafa gwiwoyin ɗaliban dake neman gurbin karatu a manyan makarantun gaba da sakandire, a ciki da wajen Najeriya.

Sarkin Zazzau Ya Yi Kiran a Tura Mata Zuwa Makaranta

A wani labarin kuma, Sarkin Zazzau mai martaba Ahmad Nuhu Bamalli ya nuna muhimmancin tura ƴaƴa mata zuwa makaranta.

Sarkin na masarautar Zazzau ya jaddada muhimmancin tura ƴaƴa zuwa makaranta su yi karatu musamman a ɓanngaren likitanci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng