An Samu Hargitsi a Majalisar Dattawa Wajen Tantance Keyamo

An Samu Hargitsi a Majalisar Dattawa Wajen Tantance Keyamo

  • An tayar da jijiyar wuya a tsakanin sanatoci a majalisar dattawa yayin tantance Festus Keyamo a matsayin minista daga jihar Delta
  • Hatsaniyar ta fara ne bayan Sanata Nwokocha ya nemi majalisar da ta dakatar da tantance Keyamo saboda wasu laifuka da ya aikata a baya
  • Ƙudirin na Nwokocha ya kawo cececkuce a tsakanin sanatoci a majalisar wanda hakan ya tilasta ta mayar da zamanta a killace

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - An samu hargitsi a majalisar dattawa wajen tantance Festus Keyamo, ministan da Shugaba Tinubu ya zaɓo daga jihar Delta.

Hargitsin ya fara ne bayan Sanatan dake wakiltar Abia ta Tsakiya, Darlington Nwokocha, ya gabatar da kuɗirin dakatar da tantance Festus Keyamo, rahoton Channels tv ya tabbatar.

An samu hargitsi wajen tantance Keyamo
An yi hatsaniya a majalisar dattawa wajen tantance Festus Keyamo Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Ƙudirin Nwokocha ya samo goyon bayan Sanatan dake wakiltar Abia ta Kudu, Sanata Enyinnaya Abaribe.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Akpabio Ya Garzaya Fadar Tinubu Bayan Hayaniya A Majalisa Kan Tanrance Keyamo

Daga nan sai shugaban majalisar dattawa ya sanya a kaɗa ƙuri'a kan ƙudirin, amma sanatocin sun samu rarrabuwar kai dangane da ƙudirin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Nan da nan sai majalisar ta ɓarke da hatsaniya ta faɗi in faɗa a tsakanin ƴan majalisar. Ana cikin hakan sai shugaban masu rinjaye na majalisar ya yi kiran da majalisar ta shiga zama na sirri.

Daga nan sai Sanata Akpabio ya miƙe ya sanar da cewa majalisar za ta shiga zamanta a sirrance, cewar rahoton Vanguard.

Laifukan da Nwokocha yake tuhumar Keyamo da su

Sanata Nwokocha ya zargi Keyamo da cin mutuncin majalisar dattawa ta tara da ƙaƙaba mata zargin cin hanci.

Keyamo, wanda babban lauya ne (SAN) ya riƙe muƙamin ƙaramin ministan ƙwadago da samar da ayyuka a ƙarƙashin gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari

Kara karanta wannan

"Shugaba Tinubu Ya Fi Sauran Shugabannin Najeriya", Cewar Jigon APC, Ya Bayyana Kwakkwaran Dalili

Nwokocha ya bayyana cewa a lokacin gwamnatin Buhari, an gayyato Keyamo a gaban majalisar domin ya yi bayani kan wani shirin ma'aikatarsa, amma sai ya yi kunnen uwar shegu da gayyatar.

Mariya Bunkure Ta Bayyana Gaban Majalisa

A wani labarin kuma, ministar da ta maye gurbin Maryam Shetty daga jihar Kano ta bayyana a gaban majalisar dattawa domin tantance ta.

Dr. Mariya Mahmoud Bunkure ta samu yabo da goyon baya daga dukkanin sanatocin da suka fito daga jihar Kano a lokacin da ake tantance ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng