Direban Mota Ya Ce Cire Tallafin Man Fetur Ne Ya Jefa Shi Aikata Fashi Da Makami

Direban Mota Ya Ce Cire Tallafin Man Fetur Ne Ya Jefa Shi Aikata Fashi Da Makami

  • Wani matashin direba ya bayyana yadda cire tallafin fetur ya jefa shi aikata mummunan laifi
  • Ya ce tsadar farashin man fetur da aka samu a Najeriya ta sanya shi faɗawa harkar fashi da makami
  • An kama matashin mai shekaru 29 a wani shago bayan gane shi da ɗaya daga cikin waɗanda ya yi wa fashi ta yi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Legas - Wani direba mai shekaru 29, ya bayyana yadda ya tsinci kansa a aikata fashi da makami.

Matashin mai suna Adeniran Jerimiah, ya bayyana cewa tsadar farashin man fetur ce ta sanya shi faɗawa mummunar sana'ar ta ƙwacen kayan jama'a.

Yadda tsadar man fetur ta jefa direba aikata fashi da makami
Direba ya ce tsadar farashin man fetur ta sanya shi faɗawa fashi da makami. Hoto: Dave Maverick
Asali: UGC

Yadda aka kama matashin dan fashin

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa an kama matashin ne a yayin da ya zo yin sayayya a wani shago a birnin Legas.

Kara karanta wannan

Kitimurmura: Soja mace ta fusata, ta harbe na gaba da ita a wurin aiki a jihar Arewa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daya daga cikin fasinjojin da ya yi wa fashin ce ta gane fuskarsa, inda daga nan ne ta sanar da mutane.

Matashin ya bayyana cewa ya yi karatun digiri a ɓangaren lissafin kuɗaɗe a jami'a.

Ya kuma ce yana haɗa kai da wasu abokanensa ne guda biyu wajen aikata ta'asa a kan duk wanda tsautsayi ya faɗawa.

'Yan sanda sun yi ram da matasa 6 bisa zargin fashi da makami a Bauchi

A wani labarin na daban da Legit.ng ta wallafa a baya, kun karanta yadda jami'an 'yan sanda suka yi ram da wasu matasa shida bisa zargin fashi da makami.

Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sandan jihar, Ahmed Wakil ya bayyana cewa mutanen da suka kama na da alaƙa da 'yan sara suka da dabanci a jihar.

Kara karanta wannan

Kyakkyawan Kurma Ya Koka Kan Rashin Samun Budurwa, Ya Ce 'Yan Mata Sun Ki Yarda Su Yi Soyayya Da Shi

Lauya ya kwana hannun 'yan sanda bayan kama shi da matar aure a Otal

Legit.ng ta yi rahoto a baya kan wani lauya da 'yan sanda suka kama bisa samunsa da matar wani da aka yi a Abuja.

Lauyan ya bayyana cewa ba bu wani abu da ya faru tsakaninsu domin kuwa ta kawo masa ziyara ne domin su tattauna wasu batutuwa da suka shafi aiki.

Ƙasurgumin ɗan daba ya miƙa kansa hannun hukumar 'yan sandan Kano

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan ƙasurgumin ɗan daba mai suna Chile Mai doki da ya miƙa kansa ga rundunar 'yan sanda jihar Kano.

Chile dai na cikin mutane 3 da rundunar ta sanya kyautar naira 300,000 ga duk wanda ya taimaka da bayanan da za a kamasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng