Sarkin Zazzau Ahmad Bamalli Ya Bukaci Iyaye Su Sanya 'Ya'ya Mata Karatu a Bangaren Kiwon Lafiya

Sarkin Zazzau Ahmad Bamalli Ya Bukaci Iyaye Su Sanya 'Ya'ya Mata Karatu a Bangaren Kiwon Lafiya

  • Mai martaba sarkin Zazzau, ya bukaci iyaye su tura 'ya'yansu mata su yi karatun likitanci
  • Ya bayyana hakan ne a yayin ƙaddamar da aiki a wani asibiti da ke Barnawa Kaduna
  • Ya ce samun ƙwararrun likitoci mata abu ne da yankin Arewacin Najeriya ke da matuƙar buƙata

Kaduna - Mai martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli, ya jaddada muhimmancin sanya 'ya'ya mata su yi karatu a ɓangaren kiwon lafiya a Arewacin Najeriya.

Ya ce samun ƙarin yawan ƙwararrun likitoci mata a yankin Arewa abu ne da ake da matuƙar buƙata.

Sarkin Zazzau ya buƙaci a sanya mata makarantun kiwon lafiya
Sarkin Zazzau Ahmad Bamalli, ya nemi a tura 'ya'ya mata su yi karatun likitanci. Hoto: Denz.b
Asali: Facebook

Ya nemi mata su yi koyi da shugabar asibitin Barnawa

Bamalli ya bayyana hakan ne a yayin ƙaddamar da aiki a asibitin kula da masu taɓin hankali da ke Barnawa Kaduna, ƙarƙashin jagorancin daraktar kula da lafiya ta asibitin, Dakta Aishatu Armiya’u.

Kara karanta wannan

"Shugaba Tinubu Ya Fi Sauran Shugabannin Najeriya", Cewar Jigon APC, Ya Bayyana Kwakkwaran Dalili

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya yabawa daraktar wacce ya kira abin koyi ga matan Arewa, duba da irin kwazon da ta yi wajen jagorantar kawo sauye-sauye a asibitin kamar yadda Daily Trust ta wallafa.

A na ta jawabin, Dakta Armiya’u ta bayyana cewa, a baya asibitin na kula da masu tabin hankali ne kawai, amma yanzu suna yin ayyukan da suka shafi kula da mata masu juna biyu, ɗaukar hoton cikin jikin ɗan Adam, da kuma wankin ƙoda.

Tsohon bidiyon El-Rufai da ya ce ba zai karɓi minista ba ya janyo surutu

A wani labarin na daban da Legit.ng ta wallafa a baya, kun karanta yadda wani tsohon bidiyo na tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya janyo cece-kuce.

An ga tsohon gwamnan a cikin tsohon bidiyon yana faɗar cewa ba adalci ba ne ya sake karɓar muƙamin minista, saboda ya taɓa riƙewa a baya.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Hallaka Manomi, Sun Sace Mata 5 Da Maza 2 a Kaduna

Mutane sun tafka muhawara biyo bayan jin sunan El-Rufai cikin waɗanda Tinubu zai naɗa ministoci duk da wancan iƙirarin da ya yi a baya.

Gwamna Uba Sani na Kaduna ya sadaukar da kaso 50% na albashinsa ga talakawan jihar

Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan sadaukar da kashi 50% na albashi da gwamnan jihar Kaduna mai ci, Sanata Uba Sani ya yi.

Gwamnan ya ce zai riƙa sadaukar da albashin ne ga wata gidauniya da za ta yi amfani da kuɗaɗen wajen ragewa talakawan jihar halin raɗadin da suke ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng