Jerin Shugabannin da Suka Shafe Shekaru Sama da 30 Suna Mulki a Kasashensu a Nahiyar Afrika
A Afirka, wasu shugabannin sun shafe sama da shekaru 30 suna mulki, wasu shugabannin kasar suna rike da madafun iko duk da kuwa sun tsufa kuma ya kamata su huta su ba wani.
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wadannan shugabanin da suka dade suna kan karagar mulki sukan ce har yanzu suna mulki ne saboda muradin ‘yan kasarsu.
A yau, wannan cikakken rahoto ya tattaro jerin sunayen shugabannin Afirka da suka fi dadewa kan karagar mulki a halin yanzu.
Ga jerin kasashen da shugabanninsu kamar haka:
1. Faure Gnassingbe, shugaban kasar Togo
Tun shekara ta 2005 Faure Gnassingbe ne ke kan shugabancin kasar Togo, kuma kafin shi mahaifinsa Gnassingbe Eyadéma ne ya yi mulki tun shekara ta 1967.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tun lokacin da ya karbi ragamar shugabancin Jamhuriyar Togo, Shugaba Faure Gnassingbe ya yi aiki don samar da sulhu na kasa da kuma yanayin siyasa cikin lumana.
A karkashin jagorancinsa, tattalin arzikin Togo na ta habaka kuma kasar ta shiga wani yanayi na zamanantarwa duk saboda jajircewarsa.
Gnassingbe na Togo a yanzu haka yana kan karagar mulki ne karo na 4 bayan mahaifinsa ya shafe shekaru 38 yana mulki.
2. Ali Bongo, shugaban kasar Gabon
Bongo mutum ne mai fuskoki da dama wanda a yanzu ke mulkin Gabon mai arzikin man fetur a matsayin wani yanki na gadonsa.
Ya kama mulki ne bayan rasuwar mahaifinsa, inda a yanzu yake rike da mukamin da ahalinsa ke rike dashi sama da shekaru 50 kenan.
3. Paul Biya, shugaban jamhuriyar Kamaru
Paul Biya ne shugaban jamhuriyar Kamaru, wanda ya shafe shekaru 41 a matsayin shugaban farar hula a kasar.
Biya ya kasance firayim minista na tsawon shekaru bakwai kafin ya zama shugaban kasa daga bisani.
An haifi Biya ne a ranar 13 ga Fabrairu, 1933 a Mvomeka'a, yankin Meyomessala. Shi da ne ga Etienne Mvondo Assam da Anastasie Eyenga Elle.
Shi ne shugaban Kamaru na biyu a tarihi. Biya ya hau kan karagar mulki ne a ranar 6 ga watan Nuwamban 1982 bayan shugaba Ahmadou Ahidjo ya yi murabus a ranar 4 ga watan Nuwamba.
4. Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, shugaban Equatorial Guinea
Theodore Obiang na Equatorial Guinea ya kwashe shekaru 44 yana shugabancin farar hula inda ya maye gurbin kawunsa.
Shugaban da aka haifa a ranar 5 ga Yuni, 1942, Teodoro Obiang Nguema, ya tsallake rijiya da baya a yunkurin juyin mulki da dama, ya samu mulkin kasar ta Afirka ta Yamma mai arzikin man fetur ne a 1979 bayan da sojoji suka ui juyin mulki.
Bayan samun mukami daga magabacinsa kuma kawunsa, Francisco Macias Nguema, ya yi wasu gyare-gyare, amma ya ci gaba da rike cikakken ikon Nguema kan al'ummar kasar.
5. Isma'il Omar Guelleh, shugaban Djibouti
Omar Guelleh shi ne shugaban jamhuriyar Djibouti, wanda ya yi shugabancin farar hula tsawon shekaru 24 da suka gabata zuwa yanzu bayan maye gurbin kawunsa.
A watan Afrilun 2021, an sake zabensa shugaba Djibouti Ismail Omar Guelleh a wa'adi na 5 da sama da kashi 98% na kuri'un da aka kada.
Ya yi mulki ne tun a shekarar 1999 lokacin da ya karbi mulki daga hannun kawunsa, shugaban kasar Djibouti na farko kuma firaministan kasar, Hassan Gouled Aptidon wanda ya yi mulki daga 1977 zuwa 1999.
Jigon APC ya gargadi sojojin Mali, Nijar da suke barazanar taran na Najeriya
A wani labarin, tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya yi wani kakkausan gargadi ga shugabannin mulkin soja a Nijar, Mali da Burkina Faso kan abin da ya bayyana a matsayin barazana ga Najeriya.
Jigon na jam’iyyar APC mai mulki ya bukaci shugabannin da suka yi juyin mulki da kada su tunzura Najeriya a yanayi irin wannan.
Bayan juyin mulkin da aka yi a jamhuriyar Nijar a baya-bayan nan da ya hambarar da shugaban kasar Mohamed Bazoum, ECOWAS, ta ba gwamnatin mulkin soji a Nijar wa'adin kwanaki bakwai da ta dawo da hambararren shugaban.
Asali: Legit.ng