“Ku Yi Tunani Sau Biyu Kafin Yi Wa Najeriya Barazana”: Fani-Kayode Ya Gargadi Mali, Burkina Faso
- Femi Fani-Kayode ya aike da sako mai zafi kuma mai muhimmanci ga wadanda suka yi juyin mulki a kasashe Nijar, Mali da Burkina Faso
- Da yake martani game da barazanar da suke yi wa Najeriya, tsohon ministan ya bukaci hukumomin mulkin soja a kasashen yammacin Afirka da su yi taka tsan-tsan
- Jigon na APC ya dage cewa Najeriya tsayayyar kasa ce mai karfin iko, kuma shugabannin juyin mulkin su yi tunani sosai kafin su yi wa Najeriya barazana da yaki
FCT, Abuja - Tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani-Kayode, ya yi wani kakkausan gargadi ga shugabannin mulkin soja a Nijar, Mali da Burkina Faso kan abin da ya bayyana a matsayin barazana ga Najeriya.
Jigon na jam’iyyar APC mai mulki ya bukaci shugabannin da suka yi juyin mulki da kada su tunzura Najeriya a yanayi irin wannan.
Bayan juyin mulkin da aka yi a jamhuriyar Nijar a baya-bayan nan da ya hambarar da shugaban kasar Mohamed Bazoum, ECOWAS, ta ba gwamnatin mulkin soji a Nijar wa'adin kwanaki bakwai da ta dawo da hambararren shugaban.
Ahir dinku da Najeriya, Kayode ga shugabannin juyin mulki
Da yake magana yayin da ake ci gaba da ririta kalaman shugaban Najeriya, Fani Kayode, a ranar Lahadi, 6 ga watan Agusta, ya wallafa wani rubutu a shafinsa na Facebook inda ya caccaki shugabannin kasashen.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce yana da yakinin cewa, jakadun da aka aika zuwa Jamhuriyar Nijar domin kawo maslahar za ta kawo mafita mai daurewa.
Daga dogon rubutun da ya yi a kuma muka gani a shafinsa, ya ce:
“Kafin ku yi mana barazana da yaki, ku yi tunani sau biyu, ku karanta tarihinmu kuma ku san mu su wanene da abin da za mu iya yi.”
Sojojin Nijar sun yi sabbin nade-nade
A tun farkon lamari, shugabannin sojin Nijar da ke rike da kasar a yanzu sun yi zabbin nade-nade a karkashin mulkinsu.
Wannan na zuwa ne yayin da suka cika kusan mako da yin juyin mulki tare da hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum.
A cikin wata sanarwar da suka fitar a ranar Juma'a da dare, sun bayyana nada Moussa Salau Barmou a kujerar babban hafsun hafsoshin sojin Nijar.
Asali: Legit.ng