An Tafka Asara Bayan Barayi Sun Kone Shaguna 20 a Tsohuwar Kasuwar Gombe

An Tafka Asara Bayan Barayi Sun Kone Shaguna 20 a Tsohuwar Kasuwar Gombe

  • Wasu ɓata-gari sun janyo ann samu asarar.miliyoyin naira a tsohuwar kasuwar Gombe bayan sun banka ma ta wuta
  • Ɓata-garin waɗanda ake kyautata zaton ɓarayi ne sun banka wa sashen teloli na kasuwar a cikin tsakar dare
  • Wutar wacce ɓata-garin suka cinna kan shagunan guda 20 ta janyo asarar maƙudan kuɗaɗe sama da N70m.

Jihar Gombe - An tafka babbar asara a wani sashe na tsohuwar kasuwar Gombe, bayan wasu ɓata-gari sun banka masa wuta.

Ɓata-garin waɗanda ake kyautata zaton ɓarayi ne dai sun cinnawa sashen kasuwar wuta a cikin tsakar dare, rahoton jaridar Aminiya ya tabbatar.

An tafka a tsohuwar kasuwae Gombe
Wutar ta lakuma kayayyaki masu daraja sosai Hoto: Aminiya.com
Asali: UGC

An ƙiyasata cewa wutar ta janyo ƴan kasuwar sun tafka gagarumar asara wacce ta kai ta maƙudan kuɗaɗe har Naira miliyan 70 (N70m).

Wutar dai ta tashi ne a layin masu ɗinki wato teloli na tsohuwar kasuwar, inda ta ƙone kimanin shaguna 20 tare da kadarori masu yawa waɗanda aka yi asarar su.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP a Arewa Ya Samu Yadda Yake So, Zai Runtumo Bashin Kuɗi Sama Da Naira Biliyan 206

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Aminu Abdulrahman, ɗaya daga cikin ƴan kasuwar da lamarin ya shafa, ya ce ya samu labarin tashin wutar ne da misalin wajem ƙarfe 1:00 na dare, bayan an buga masa waya.

Aminu ya bayyana cewa ya yi asarar kekunan ɗinki har guda 10 da wasu kayayyaki masu daraja, waɗanda kuɗinsu sun kai N2.5m.

Wani ɗan kasuwar mai Sani Idris, ya bayyana cewa abin da ya faru abin takaici ne domin an janyo musu asara ba ƴar kaɗan ba.

Hukumomi sun tabbatar da aukuwar lamarin

Da yake magana kan wutar da ta tashi, shugaban ƙungigar teloli na kasuwar, Abu Safwan Muhammad Tukur, ya bayyana kaduwarsa kan abun takaicin da ya auku akan telolin.

Abu Safwan bayyana cewa mambobinsu da yawa sun yi gagarumar asaraɓta dukiya mai tarin yawa wacce ta kai ta N70m.

Shugaban ƙungiyar telolin ya buƙaci hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Gombe (SEMA) da ta gaggauta kawo musu agaji.

Kara karanta wannan

Ta Fasu: Jiga-Jigan APC Sun Tona Asirin Wike, Sun Faɗi Dalilinsa Na Haɗe Wa da Shugaba Tinubu

Gobara Ta Lakuma Shaguna 12 a Adamawa

A wani labarin kuma, wata gobara da ta shi a babbar kasuwar jihar Adamawa a bkrnin Yola ta lalata shaguna 14.

Gobarar dai ta tashi ne a dalilin fashewar wani tulun iskar gas wanda ya janyo asarar dukiya mao tarin yawa a cikin shagunan da lamarin ya ritsa da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng