Ana Ta Kokarin Daukar Mataki a Kansu, Sojojin Juyin Mulki a Nijar Sun Yi Sabbin Nade-Nade
- Yayin da ake kokarin kwace mulki daga hannun sojojin Nijar, sun yi sabbin nade-nade a shugabancin kasar
- An nada ministan tsaro da kuma sauran mukamai masu muhimmanci game da tsaron kasar ta Nijar
- Sun bayyana cewa, suna shirye da daukar duk wani kalubalen farmaki daga sojojin ECOWAS a kowane lokaci
Yamai, Nijar - Shugabannin sojin Nijar da ke rike da kasar a yanzu sun yi zabbin nade-nade a karkashin mulkinsu.
Wannan na zuwa ne yayin da suka cika kusan mako da yin juyin mulki tare da hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum.
A cikin wata sanarwar da suka fitar a ranar Juma'a da dare, sun bayyana nada Moussa Salau Barmou a kujerar babban hafsun hafsoshin sojin Nijar.
Yadda sauran mukamai suka kasance a sojin Nijar
Hakazalika, sanarwar ta bayyana nada Kanal Amirou Kader zai ya zama mataimakinsa, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A bangare guda, Manjo Kanar Sani Kiaou ne zai kasance sabon shugaban rundunar sojin kasa a kasar.
Kanar Abdoutahamane Zakata zai rike mukamin mataimakin shugaban rundunar sojin kasan Nijar.
A bangaren ofishin ministan tsaron kasar, sanarwar ta ce an nada Janar Sani Kache don kula da wannan fannin.
A shirye muke mu tunkari sojojin ECOWAS, inji sojin Nijar
Ya zuwa yanzu, sojojin Nijar sun ce a shirye suke su tunkari duk wani kalubale na farmaki daga sojojin kungiyar ECOWAS zuwa kasarsu.
Tun bayan hambarar da gwamnatin Bazoum, sojojin Nijar suka samu gargadi daga kungiyar raya kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS) da bayanai masu tsauri.
Kungiyar ta yi barazanar mai da Nijar saniyar ware tare da kakaba mata takunkumin da ka iya jawo sartse ga ci gaban mulkin na soji.
Hakazalika, ECOWAS ta ce za ta yi amfani da karfin soja don tabbatar da mai da Bazoum kan mulkin Nijar.
Sanatocin Najeriya sun ce basu amince a tura sojin kasar su yaki na Nijar ba
Sai dai, ECOWAS ta samu tsaiko yayin da Sanatoci a Najeriya suka ce ba za su amince a tura sojin Najeriya zuwa Nijar ba.
A cewar rahoto, sama da 90% na Sanatocin ne suka bayyana rashin amincewarsu da yunkurin Shugabancin Tinubu.
Amma, majalisa ta bayyana yin Allah wadai da aikin da sojoji suka yi na kifar da mulkin Mohammed Bazoum.
Asali: Legit.ng