Bosun Tijani Ya Nemi Afuwar Sanatocin Kan Kiransu da Sunan ‘Wawaye’ a 2021 a Shafin Twitter

Bosun Tijani Ya Nemi Afuwar Sanatocin Kan Kiransu da Sunan ‘Wawaye’ a 2021 a Shafin Twitter

  • Daya daga cikin wadanda Tinubu ya dauko a ba minista ya gamu da titsiyen sanatoci a lokacin da ake tantance shi
  • An tono masa bayanan da ya taba yi a lokacin da yake ganiyar Twitter, inda ya kira sanatocin wawaye
  • Ya zuwa yanzu, ya nemi gafara a wurinsu, kuma an tantance shi ya wuce ya yi tafiyarsa bayan hada zufa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Bosun Tijani, daya daga wadanda Tinubu ya mika sunayensu majalisa don a tantance su zama ministoci, ya nemi afuwar Sanatocin bisa kiransu da wawaye a wani sakon da ya wallafa a Twitter a shekarar 2021.

A ranar Asabar, Tijani, wanda yake Shugaba kuma wanda ya kafa CCHub, ya bayyana a gaban majalisar dattijai don a tantance matsayin minista, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

An Taso Tinubu, Ana Neman a Cire Tsohon Gwamna Daga Ministoci Kamar Shetty

Jigon siyasar wanda yake dan asalin jihar Ogun ne ya nemi afuwar ‘yan majalisar bisa kiransu da sunan da bai dace ba.

Yadda aka titsiye ministan Tinubu a majalisar dattawa
An titsiye ministan Tinubu a majalisar dattawa | Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban marasa rinjaye a majalisar dattawa, Simon Nwadkon ne ya karanto abin da Tijani ya rubuta a shafin na Twitter.

A rubutun nasa na Twitter da ya wallafa a 2021, Tijani ya caccaki salon tantancewa da tabbatar da nadin mukaman siyasa da majalisar dattawa ke yi.

Nwadkon ya tambayi Tijani shin ko shi ne ya rubuta a shafinsa Twitter yana sukar Sanatoci a wancan lokacin, rahoton Daily Post.

Bayan tambayoyin Nwadkon, wasu Sanatoci sun tashi tsaye don yin muhawara game da sahihancin wanda aka zaba ya zama ministan.

Bayanin da ya yi

Sai dai a karshen gabatar da jawabai, Godswill Akpabio, shugaban majalisar dattawa, ya bukaci Tijani da ya nemi gafarar sanatocin kan kalaman da ya yi maras dadi a kansu a Twitter.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Fadi Dalilin Ƙin Halartar Taron da Ganduje Ya Zama Sabon Shugaban APC

Da yake mayar da martani, Tijjani ya nemi afuwar Sanatocin da ‘yan Najeriya baki kan kalaman da ya yi a shafukan sada zumunta gaba daya.

Ya ce kalaman nasa ba wai don komai ya yi su sai don nuna kishi da damuwarsa a kan Najeriya.

Sanatocin Najeriya sun yi maganar karshe kan batun tura sojojin Najeriya su yaki na Nijar

A wani labarin, Sanatocin Najeriya sun yi watsi da bukatar da Shugaba Bola Tinubu na kai sojojin Najeriya zuwa Nijar don tabbatar da tafarkin dimokradiyya.

Tinubu ta hannun ECOWAS ya ce zai tura sojojin Afrika domin su dawo da Mohamed Bazoum na Nijar kan mulki.

Ya zuwa yanzu, majalisar ta yi Allah wadai da abin da ya faru a Nijar, amma ba za ta tura sojin Najeriya ba

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.