A Duba Dai: Sanatocin Arewa Ba Su Yarda Tinubu Ya Shiga Yaki Da Kasar Nijar Ba
- Sanatocin da su ka fito daga mazabun yankin Arewa su na da ja game da shiga yaki da kasar Nijar
- Abdulrahman Suleiman Kawu Sumaila ya bayyana matsayar su a karkashin jagorancin Abdul Ningi
- ‘Yan majalisar su na ganin babu dalilin ayi amfani da karfin tuwo idan dai akwai damar ayi sulhu
Abuja - Sanatocin da su ka fito daga jihohin Arewacin Najeriya, ba su gamsu da maganar daukar makami a kan sojojin Jamhuriyyar Nijar ba.
Shugabannin kungiyar ECOWAS su na neman yakar Nijar a sakamakon juyin mulki da sojoji su ka yi, Tribune ta ce wasu Sanatoci su na da ja a kai.
Wakilan jihohin Arewa a majalisar dattawa, sun fadawa Mai girma shugaban Najeriya cewa ya sake nazari kan maganar shiga Nijar da yaki.
Sulhu alheri ne
Daily Trust ta ce ‘yan majalisar Arewa a karkashin Abdul Ningi su na ganin ba matakin da ya dace a dauka shi ne yin sulhu da sojojin tawayen.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sanata Abdulrahman Suleiman Kawu Sumaila wanda shi ne Mai magana da yawun bakin Sanatocin Arewa a majalisar dattawa, ya fitar da jawabi.
Da yake magana ranar Juma’a a Abuja, Abdulrahman Kawu Sumaila ya ce matsayarsu ita ce a bi matakin siyasa a wajen magance rikicin.
Jawabin Abdulrahman Kawu Sumaila
“Ba mu goyon bayan a kai ga amfani da karfin bindiga sai dai idan an yi amfani da duk matakan da aka ambata
Dalili kuwa saboda irin abin da zai biyo baya na kashe-kashen ‘yan kasar da ba su da laifin komai.
Baya ga haka, kusan jihohin Arewa bakwai su ka yi iyaka da Nijar, su ne: Sokoto, Kebbi, Katsina, Zamfara, Jigawa, Yobe da Borno, abin zai shafe su.
Mu na kuma sane da halin da ake ciki a Mali, Burkina Faso da Libya, wanda zai iya shafan wadannan jihohin Arewan, idan aka yi amfani da soji.
- Abdulrahman Suleiman Kawu Sumaila
Sumaila ya ba abokan aikinsa shahara su yi hattara wajen amfani da sashe na 5 na karamin sashen (4) (a) da (b) a kundin tsarin mulki da ya halatta yaki.
Takardar shugaban kasar ta je Majalisa
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aikowa majalisar dattawa takardar neman izinin tura dakaru zuwa makwabta a karkashin kungiyar ECOWAS.
A haka aka rahoto Shehu Sani wanda ya je majalisa tsakanin 2015 da 2019 ya na ba Sanatoci shawara su duba abin da zai biyo bayan yakar Nijar.
Asali: Legit.ng