'Yan Daba Sun Afka Wa Shugabannin APC, Sun Raunata Mutane Da Barnata Kayayyaki

'Yan Daba Sun Afka Wa Shugabannin APC, Sun Raunata Mutane Da Barnata Kayayyaki

  • 'Yan daba sun kai farmaki kan shugabannin jam'iyyar APC tare da raunata da dama a jihar Ekiti
  • Yayin harin an yi asarar dukiyoyi na miliyoyin Nairori inda harin ya rutsa da shahararren dan kasuwa Cif Bode Olayinka
  • Harin bai rasa nasaba da zabukan da ke tafe na kananan hukumomi a watan Disamba da za a yi a jihar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Jihar Ekiti - Akalla mutane hudu ne suka samu raunuka yayin da 'yan daba su ka kai farmaki kan shugabannin APC a jihar Ekiti.

Daga cikin wadanda suka samu raunukan akwai shahararren dan kasuwa Cif Bode Olayinka.

'Yan daba sun kai farmaki kan 'yan APC a jihar Ekiti kan zaben kananan hukumomi
Yan Daba A Jihar Ekiti Sun Afka Wa Shugabannin APC Tare Da Raunata Da Dama. Hoto: The Eagle Online.
Asali: Facebook

'Yan daban sun kuma lalata dukiyoyin al'umma ta miliyoyin Nairori a karamar hukumar Efon da ke jihar.

An kai harin ne don rufe bakin sauran 'yan takara a zaben

Harin kamar yadda jaridar Punch ta tattaro bai rasa nasaba da zaben kananan hukumomi da za a yi a watan Disamba, New Telegraph ta tattaro.

Kara karanta wannan

Abba Gida Gida Ya Ce Ya Na Bukatar Biliyan 6 Don Wadatar Da Makarantun Kano Da Kujerun Zama, Ya Koka Da Mulkin Ganduje

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Daya daga cikin wadanda abin ya rutsa da su, Mista Olaitan Olayinka ya ce tsagerun sun zo fiye da 20 da makamai inda suka far musu yayin da suke hutawa a kofar gida a ranar Litinin.

Ya ce ana zargin wani babban dan siyasa a yankin da hannu a rikicin don rufewa sauran abokan hamayyarsa baki.

Ya bayyana yadda 'yan daban suka kai musu farmaki kan zabe

Ya ce:

"Na yi ritaya a aikin gwamnati, ina neman takarar kujerar shugaban karamar hukuma, amma dan siyasa ya sa an kai mana farmaki.
"Sun ce ba sa son kowa ya tsaya takara idan ba wanda suke so ba, ni kuma na ce zan tsaya takara kuma zan yi nasara.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar, Sunday Abutu ya ce an kama babban dan siyasar kuma an gurfanar da shi a gaban kotu, Head Topics ta tattaro.

Kara karanta wannan

Sifetan 'Yan Sanda Ya Tura Muhimmin Sako Ga NLC Da TUC, Ya Ba Su Shawara

Gini Ya Rufta Kan Shugaban Alkalan Jihar Ekiti A Ofishinsa

A wani kabarin, shugaban alkalan jihar Ekiti, Oyewole Adeyeye ya tsallake rijiya ta baya yayin da ginin babbar kotun jihar ya danne shi.

Rahotanni sun tabbatar cewa ginin ya danne shi yayin da ya ke cikin ofis a ranar Laraba 12 ga watan Yuli.

Yanzu haka shugaban alkalan jihar na kwance a wani asibiti inda ya ke samun kulawa na musamman.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.