‘Yan Kasuwa Sun Nuna Abin da Zai Jawo Man Fetur Ya Sauko Daga N620 a Farat Daya

‘Yan Kasuwa Sun Nuna Abin da Zai Jawo Man Fetur Ya Sauko Daga N620 a Farat Daya

  • Wani shugaba a kungiyar IPMAN ya yi hasashen farashin da fetur zai koma idan aka gyara matatu
  • A maimakon sayen man fetur a kan fiye da N600, Mike Osatuyi ya ce farashin zai ragu da N70
  • Gwamnati za ta daina biyan kudin jirgi da na sauke kaya idan aka daina kawo fetur daga ketare

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Abuja - ‘Yan kasuwan da ke harkar mai sun shaida cewa idan aka fara tace danyen mai a cikin gida, farashin da ake sayen man fetur zai ragu.

‘Yan kasuwan sun ce za a samu saukin akalla N70 a kan kowace lita idan matatun Najeriya su ka fara aiki, Jaridar Punch ta fitar da rahoton nan.

Shugaban sashen aikaca-aikace na kungiyar IPMAN, Mike Osatuyi, ya yi wannan bayani da yake magana kan muhimman gyara matatun kasar.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Hanyoyi 4 na kare kai daga fadawa ta'addanci bayan cire tallafin man fetur

Fetur
Jirgi ya dauko fetur Hoto: cen.acs.org
Asali: UGC

Kyau a gama gyaran da wuri

Duk da an bada kwangilar gyaran wasu matatun, Mista Mike Osatuyi ya shaida cewa za a amfana kwarai da gaske idan aka fara tace mai da wuri.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Saboda haka ne ‘dan kasuwan yake so ayi maza a kammala gyaran matatun domin a huta da wahalar shigo da taceccen mai daga kasashen waje.

"An bada kwangilar tun kafin sabuwar gwamnatin nan ta shga ofis. IPMAN ba ta san yanayin kwangilar ba.
Amma idan matatunmu su na aiki, za su rage kashe kudin jigila ta jirgi da kudin dauko mai ta cikin jiragen ruwa.
Akalla N60 ko kuwa N70 zai ragu a farashin kowane lita idan matatun su ka fara yin aiki."

- Mike Osatuyi

An rage wahalar inshora da cin lokaci

A rahoton Linda Ikeji, an ji cewa gyaran matatun da gwamnati ta mallaka zai taimakawa matasan kasar wajen samun aiki, a rage zaman banza.

Kara karanta wannan

Masu Phd 3: Kwararewa da matakin ilimin ministocin da Tinubu ya nada

Osatuyi ya ce za a rage batar da kudi da sunan biyan inshora idan aka farfado da matatun man, sannan a rage bata lokaci kuma a daina hayar jirage.

Soke tallafin fetur da karya darajar Naira

Watanni biyu da zama Shugaban Najeriya, Bola Tinubu yana fuskantar fushin al'ummarsa, an ji labari 'yan kwadago sun fara yi masa zanga-zanga.

A lokacin yakin zabe, Bola Tinubu ya sha alwashin cire tallafin fetur ko da jama’a za su yi zanga-zanga, yanzu dai wasu na kuka da tsare-tsaren da ya kawo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng