Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Malaman Coci Biyu a Jihar Neja

Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Malaman Coci Biyu a Jihar Neja

  • Wasu malaman cocin Katolika a jihar Neja sun shiga hannun masu garkuwa da mutane da safiyar ranar Alhamis, 3 ga watan Agusta, 2023
  • Bayanai sun nuna yan bindigan sun sace Fastocin biyu a cikin gidansu da ke garin Gyedna a karamar hukumar Tafa
  • Jami'in hulɗa da jama'a na rundunar yan sandan jihar ya ce tuni aka tura dakarun sashin dabaru zuwa wurin da lamarin ya faru

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Niger - Wasu 'yan bindiga da ake zaton 'yan fashin jeji ne sun yi garkuwa da Malaman Cocin St Luke’s Catholic Church, Gyedna da ke gundumar Garam a ƙaramar hukumar Tafa, jihar Neja.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa maharan sun sace Fastocin guda 2, Fasto Paul Sanogo da Fasto Seminarian Melchior, a gidansu da ke Gyedna da sanyin safiyar ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Kotu Ta Tura Shugabar Masu Addinin Gargajiya Gidan Yari a Ilorin Kan 'Cin Mutuncin' Shehin Malamin Islama

Harin yan bindiga a jihar Neja.
Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Malaman Coci Biyu a Jihar Neja Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Mazauna yankin sun bayyana cewa masu garkuwan sun buɗe wuta a kan iska na tsawon sa'a guda domin tsorata mutane kafin daga bisani suka sace manyan Fastocin.

Babban Cocin Katolika ta tabbatar da sace Fastocin 2

Bishof din Cocin Katolika da ke Minna, babban birnin jihar Neja, Rabaran Dakta Martin Igwe Uzoukwu, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani saƙo da ya aike wa mabiyansu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ce Fastocin da yan bindigan suka yi garkuwa da su, suna wa'azi ne a cocin Katolika (St Luke’s Catholic) ta garin Gyedna.

A saƙon, babban malamin Katolika ya ce:

"A madadin babban malamin mu na cocin Katolika ta Minna, Rabaran Sylvester Luka Gopep, ina roƙon ku sanya Paul Sanogo da Seminarian Melchior cikin Addu'a, waɗanda aka yi garkuwa da su ranar 3 ga watan Agusta, a Gyedna."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Farmaki Gidan Gonan Sanata a Arewa, An Rasa Rai

"Fr Paul Sanogo (M.Afr) da Seminarian Melchior Fastoci ne masu wa'azi a Cocin Katolika da ke Gyedna, jihar Neja, muna fatan Allah ya ji kokenmu ya dawo mana da su cikin ƙoshin lafiya."

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Da aka tuntubi kakakin rundunar ’yan sandan jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda Dailypost ta rahoto.

Ya ce tuni aka aike da tawagar dakarun sashin dabara karkashin jagorancin DPO mai kula da yankin Tafa zuwa wurin da lamarin ya faru.

Yan Bindiga Sun Kai Hari Gidan Gona Sanata a Jihar Kwara, Sun Halaka Manaja

A wani rahoton kuma Wasu yan bindiga da ake kyautata zato masu garkuwa da mutane ne sun kai hari gidan gonar tsohon Sanatan Kwara ta kudu.

Rahoto ya nuna cewa maharan sun halaka Manajan da ke kula da gidan gonan kuma ɗan uwan tsohon Sanatan yayin harin na ranar Litinin.

Kara karanta wannan

El-Rufai Da Sauran Jerin Sunayen Ministocin Da Majalisa Za Ta Tantance a Yau Talata

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262