Kungiyoyin Kwadago Sun Janye Yajin Aikin Da Su Ke Shirin Farawa

Kungiyoyin Kwadago Sun Janye Yajin Aikin Da Su Ke Shirin Farawa

  • Ƙungiyoyin ƙwadago sun dakatar da batun shiga yajin aikin da su ke shirin tsunduma na gama gari a faɗin ƙasar nan
  • Ƙungiyoyin ƙwadagon sun dakatar da shiga yajin aikin ne bayan sun tattauna da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a Villa
  • Ƙungiyoyin ƙwadagon sun bayyana cewa samun tabbaci kan biyan wasu buƙatun su da suka samu daga wajen Shugaba Tinubu ya sanya suka dakatar da fara yajin aikin

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - ƙasa da sa'o'i 24 bayan ƙungiyoyin ƙwadago sun tsunduma cikin zanga-zangar gama gari a faɗin ƙasar nan, ƙungiyoyin ƙwadagon sun sanar da janye yajin aikin da su ke shirin farawa.

Shugaban ƙungiyar ma'aikata (TUC), Festus Osifo, shi ne ya bayyana hakan a yayin wata tattaunawa da gidan talbijin na Arise News, da safiyar ranar Alhamis 3 ga watan Yulin 2023, cewar rahoton The Punch.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu Ya Fara Shawo Kan Shugabannin Kwadago a Taron Villa, Bayanai Sun Fito

Kungiyoyin kwadago sun fasa shiga yajin aiki
Shugabannin kungiyoyin kwadago tare da Shugaba Tinubu Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Dalilin janye yajin aikin

Ya bayyana cewa shugabannin ƙungiyoyin ƙwadagon waɗanda suka gana da Shugaba Tinubu, sun samu tabbaci kan wasu daga cikin buƙatun da suka gabatar waɗanda su ke buƙatar aiwatarwa da gaggawa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya yi bayanin cewa sun dakatar da fara yajin aikin ne saboda wannan tabbacin da suka samu daga ɓangaren gwamnatin tarayya.

A ranar Talata ne dai ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa ta sanar da cewa za ta gudanar da zanga-zangar gama gari da ta shirya bayan gudanar da wani zama da wakilan gwamnatin tarayya.

Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC), Kwamared Joe Ajaero, ya yi nuni da cewa zaman da suka yi da wakilan na gwamnatin tarayya bai haifar da wani ɗa mai ido ba, wanda zai sanya su dakatar da abinda suka shirya gudanarwa.

Sun bayyana cewa a shirye su ke domin jajircewa wajen wakiltar ma'aikatan Najeriya da kare muradu da buƙatun al'umma.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Sabon Farmaki a Jihar Arewa, Sun Yi Awon Gaba Da Mutane Masu Yawa

Abinda Mu Ka Tattauna Da Shugaba Tinubu - Shugabannin Kwadago

A wani labarin kuma, shugabannin ƙungiyoyin ƙwadago sun yi bayanin abinda suka tattauna da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Shugaban ƙungiyar ƙwadagon na ƙasa (NLC), kwamred Joe Ajaero ya ce shugaban Najeriyan ya tabbatarwa al’ummar kasar nan cewa gwamnatinsa za ta tabbatar an gyara matatar mai a bana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng