Hafsoshin Tsaron Kasahen Afirka Sun Sa Labule a Abuja Kan Juyin Mulkin Nijar

Hafsoshin Tsaron Kasahen Afirka Sun Sa Labule a Abuja Kan Juyin Mulkin Nijar

  • Hafsoshin tsaron ƙasashen yammacin Afirka na gana wa a hedkwatar tsaro da ke Abuja kan juyin mulkin da ya auku a jamhuriyar Nijar
  • Taron na gudana ƙarƙashin jagorancin shugaban hafsoshin tsaron ƙungiyar ECOWAS kuma babban hafsan tsaron Najeriya, Christopher Musa
  • Kungiyar bunkasa tattalin arzikin ƙasashen yammacin Afirka (ECOWAS) ta bai wa sojojin Nijar wa'adin mako ɗaya su maida mulki ga Bazoum

FCT Abuja - Manyan hafsoshin tsaro daga ƙasashen yammacin Afirka sun dira hedkwatar tsaro ta ƙasa da ke Abuja domin halartar taro na musamman kan juyin mulkin Nijar.

Wannan taro ya ƙunshi manyan wakilai daga ƙasahen yammacin Afirka kuma zasu maida hankali ne kan abinda ke faruwa dangane da juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar Nijar kwanan nan.

Taron manyan hafsoshin tsaron yammacin Afirka.
Hafsoshin Tsaron Kasahen Afirka Sun Sa Labule a Abuja Kan Juyin Mulkin Nijar Hoto: dailytrust
Asali: UGC

Wakilin Daily Trust da ke ɗauko rahoton abinda ke wakana a wurin taron, ya gano cewa ba bu kowa a kujerun da aka ware wa hafsoshin tsaron ƙasashen Mali, Guinea Bissau, Nijar da Burkina Faso.

Kara karanta wannan

Dakarun Soji Sun Kai Farmaki Sansanin 'Yan Ta'adda a Cikin Daji, Sun Samu Gagarumar Nasara

Haka nan kuma manyan hafsoshin tsaron da aka hanga sun hallara a ɗakin taron sun ƙunshi na ƙasashen Togo, Sierra Leone, Senegal, Najeriya, Ghana, Liberia, Guinea, Gambia, Cote’Divoire, Cabo Verde da jamhuriyar Benin.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Taron na gudana yanzu haka karƙashin jagorancin shugaban hafsoshin tsaron ƙungiyar ECOWAS kuma babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, The Nation ta tattaro.

ECOWAS ta bai wa sojojin Nijar wa'adin mako guda

A ranar Lahadin da ta gabata ne kungiyar bunƙasa tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS ta bai wa sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Nijar wa’adin mako guda.

Kungiyar ta buƙaci su maido da tsarin mulkin dimokuradiyya a kasar cikin wannan wa'adi ko kuma su dauki matakin soji a kansu.

Tun ranar Laraba da ta shige, jami'an tsaron da ke gadin fadar shugaban kasar Nijar suka tsare shugaban Mohammed Bazoum a fadarsa.

Kara karanta wannan

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Allah Ya Yi Wa Tsohon Shugaban Ƙasa Rasuwa a Nahiyar Afirka

A ranar Juma'a kuma sojojin suka sanar da Janar Abdourahamane Tchiani, shugaban masu gadin shugaban kasa a matsayin sabon shugaban kasar.

Jirgin Sama Mai Saukar Ungulu Ya Fado a Jihar Legas

A wani rahoton kuma kun ji cewa An samu hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a birnin Ikeja, babban birnin jijar Legas dake yankin Kudu maso Yamma.

Kakakin hukumar bincike ta NSIB, Tunji Oketunbi, ya tabbatar da aukuwar hatsarin jirgin saman na ranar Talata da rana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262