"Ko Kwandala Ba a Ceto Ba" NLC Ta Kalubalanci Ikirarin Tinubu Na Tara N1rn

"Ko Kwandala Ba a Ceto Ba" NLC Ta Kalubalanci Ikirarin Tinubu Na Tara N1rn

  • Ƙungiyar kwadugo ta soki kalaman shugaba Tinubu cewa zuwa yanzu gwamnati ta ceto kuɗi Naira Tiriliyan ɗaya daga cire tallafin fetur
  • Shugaban NLC, Kwamaret Joe Ajaero, ya bayyana cewa wakilan FG sun faɗa musu ko kwandala ba a tara ba tun da aka cire tallafin
  • A yau Laraba, 2 ga watan Agusta, 2023, ƙungiyoyin kwadugo suka fara zanga-zanga kan wahalhalun da suka biyo baya

FCT Abuja -Kungiyar kwadugo (NLC) ta caccaki shugaban kasa Bola Tinubu kan ikirarin cewa an ceto Naira Tiriliyan 1 tun bayan da gwamnatinsa ta dakatar da biyan tallafin man fetur.

Idan baku manta ba a cikin jawabinsa ga 'yan ƙasa ranar Litinin, shugaban Tinubu ya ce an ceto jimillar Naira Tiriliyan ɗaya tun lokacin da aka cire tallafin, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Bayan Taro a Aso Villa, NLC Ta Yi Magana Kan Janye Zanga-Zanga da Shiga Yajin Aikin da Ta Shirya a Najeriya

Shugaban NLC na jagorantar zanga-zanga a Abuja.
"Ko Kwandala Ba a Ceto Ba" NLC Ta Kalubalanci Ikirarin Tinubu Na Tara N1tr Hoto: Nigeria Labour Congress HQ
Asali: Facebook

"A watanni biyu da muka karɓi mulki, mun tara zunzurutun kuɗi N1tr da aka saba kashewa da sunan tallafin mai, wanda wasu tsirararun 'yan fasa kwauri da masu damafara ke amfana," in ji Tinubu.

Ko Kobo gwamnati ba ta ceto ba - NLC

Amma da yake jawabi a wurin zanga-zanga, shugabn NLC na ƙasa, Joe Ajaero, ya ce kwamitin da FG ta kafa domin tattaunawa da 'yan kwadugo ya faɗa musu ba a tara ko Kobo ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kwamaret Joe Ajaero ya bayyana cewa ko Kwandala gwamnatin Tinubu ba ta tara ba bayan tsame hannu daga biyan kuɗin tallafin man fetur watanni 2 da suka shige.

Shugaban NLC ya ce:

"Shugaban kasa ya yi magana game da Naira tiriliyan 1 da aka ceto, kwamitin da muka zauna da shi ya shaida mana cewa kawo yanzu babu wani Kobo da aka ceto."

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: FG Da NLC Sun Fara Tattaunawa Kan Shirin Rage Radadi Na Tinubu Bayan Cire Tallafin Man Fetur, Bayanai Sun Fito

A jawabin wurin rantsarwa ranar 29 ga watan Mayu, shugaba Tinubu ya bayyana janye tallafin man fetur, wanda hakan ya sa aka kara farashin man fetur daga N195 zuwa N540 kowace lita.

Haka zalika, a farkon watan Yuli da ya gabata ne aka kara farashin zuwa Naira 617 kan kowace lita, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Gwamna Radda Ya Rantsar da Sabbin Kwamishinoni a Katsina, Ya Raba Ma'aikatar Ilimi

A wani rahoton kuma Gwamnan Katsina ya rantsar da sabbin kwamishinoni 20 da kuma mashawarta na musamman 18 ranar Talata.

Radda ya kuma raba ma'aikatar ilimi zuwa gida biyu, ma'aikatar ilimi mai zurfi, fasaha da aikin yi da kuma ma'aikatar ilimin matakin farko da Sakandire.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262