Matashi Ya Tsere A Gidan Kaso Watanni 4 Kafin Gama Wa'adinsa, An Yanke Masa Shekaru 40 Bayan Ya Shiga Hannu
- Wani matashi ya ba da mamaki yayin da ya tsere daga gidan kaso ana saura watanni hudu ya fita
- Matashin mai suna Shunekndrick Huffman dan shekaru 21 ya tsere tare da aikata wasu laifuka a cikin gari
- Daga bisani hukumomi sun kama shi tare da yanke masa hukuncin daurin shekaru 40 a gidan kaso
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wani matashi ya tsere daga gidan kaso na Mississippi da ke Amurka kafin daga bisani a sake kama shi.
Wanda ake zargin Shunekndrick Huffman mai shekaru 21 ya tsere ne a 2022 amma ya sake aikata wani laifi har aka sake kama shi, Legit.ng ta tattaro.
Abin takaici saura watanni hudu ya kammala wa'adinsa a gidan kason, amma bayan kama shi an yanke masa hukuncin daurin shekaru 40.
An kama Huffman yana fashi a wani gida inda ya yi garkuwa da mutanen gidan har na tsawon sa'o'i.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An bayyana yadda matashin ya tsere bayan aikata laifuka
Huffman ya kuma saci mota yayin fashin daga wurin mutanen inda ya yi hatsari da ita yayin gudu, cewar Daily Mail.
Daga bisani an kama matashin inda ake zargin shi da laifuka guda biyu kuma ya amince da aikata su.
A yanzu haka kotu ta yanke masa hukuncin zaman gidan kaso shekaru 40, wannan labari ya ba mutane mamaki inda suke cewa meye yasa ba zai hakura wa'adinsa ya cika na watanni hudu ba.
Daily Loud ta sake wallafa labarin a shafinta na Twitter.
Martanin mutane a kafar Twitter bayan yanke hukuncin shekaru 40.
@Irunnia:
"Waye yake ba wa wadannan shawara? Ka yi shekaru da dama saura watanni kadan, ka yi kokarin tserewa."
@dr_dripto:
"Dan uwa ka yi kuskure sau da dama."
Ma’aikacin Banki Ya Bayyana Yadda Ya Yi Amfani Da PoS Da Aka Yi Kutse Wajen Cire Kudi Sau 5 Daga ATM Din Kwastoma
@abazwhyllzz:
"Omo, me ya matse ka haka da ka dauki wannan mataki."
An Maka 'Group Admin' A Kotu Kan Zargin Cire Mamba A 'WhatsApp', An Kara Masa Girma
A wani labarin, wani matashi ya maka mai gudanar da rukunin manhajar WhatsApp a kotu kan cire shi a 'Group'.
Matashin mai suna Herbert Baitwababo ya maka mutumin a kotu saboda ya ce sai da ya biya kafin aka saka shi a 'Group' din.
Alkalin kotun ya yanke hukunci inda ya ce a mayar da Herbert tare da kara masa girma a rukunin.
Asali: Legit.ng