Anambra: Sojoji Sun Kai Farmaki Mafakatar Yan Ta'addan IPOB, Sun Kama 5
- Dakarun sojin Najeriya da haɗin guiwar sauran hukumomin tsaro sun ragargaji mayaƙan kungiyar IPOB/ESN a jihar Anambra
- Daraktan yaɗa labarai na hukumar sojin Najeriya, Nwachukwu, ya ce jami'an sun kwamuso 'yan ta'adda 5 a farmakin na ranar Litinin
- Sai dai ya ce sojoji 5 da yan sanda biyu sun samu raunuka sakamakon bama-bama da yan tada ƙayar bayan suka ɗana
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Anambara - Hukumar Sojin Najeriya ta bayyana cewa rundunar hadin gwiwa ta jami’an tsaro ta kai samame sansanin ‘yan awaren Biafra (IPOB) da mayaƙanta (ESN) a jihar Anambra.
Jaridar Daily Trust ta ce yayin wannan samame, jami'an tsaron sun yi nasarar damƙe hatsabiban mayaƙa 5 na haramtacciyar ƙungiyar IPOB.
Daraktan yaɗa labarai na hukumar Soji, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai.
Ya ce dakarun soji sun yi fata-fata da sansanin 'yan ta'adda, wanda ke cikin ƙurmin daji a yankin ƙauyen Orsumoghu, ƙaramar hukumar Nnewi ta Kudu, ranar Litinin.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Daraktan ya ce:
"An kai farmakin ne ranar Litinin 31 ga watan Yuli lokacin da dakarun soji suka samu labarin ayyukan yan ta'addan waɗanda ke tilasta dokar zaman gida a Onitsha, Nnewi da Iheme Obosi a Anambra da wata kasuwa a Enugu."
"Wannan wani ɓangare ne na kokarin kawo karshen dokar zaman gida ta kwana biyu da IPOB da tawagar mayaƙanta ESN suka sanya."
Jami'an tsaro sun samu raunuka a farmakin
Nwachukwu ya ƙara da cewa dakarun sojin sashi na 82 da haɗin guiwar sauran hukumomin soji, 'yan sanda da sauransu ne suka samu nasarar lalata maɓoyar IPOB ɗin a Anambra.
A cewarsa, jami'an tsaron sun tashi sansani da wurin ɗaukar horon mayaƙan IPOB/ESN a dajin Orsomoghu wanda ya haɗa jihohin Anambra da Imo.
A rahoton The Cable, kakakin sojin ya ci gaba da cewa:
“Abin takaici, sojoji biyar da ‘yan sanda biyu sun samu raunuka daban-daban daga bama-baman da barayin suka tayar."
“A yayin samamen, sojojin sun fatattaki ‘yan kungiyar ta IPOB da ke Ekeututu, Orsomoghu, Lilu da kuma Mother Valley."
Tsohon Shugaban Ƙasar Ivory Coast, Konan Bedie, Ya Rasu Yana da Shekaru 89
A wani rahoton kuma Tsohon shugaban ƙasar Ivory Coast, Henri Konan Bedie, ya kwanta dama yana da shekaru 89 a duniya.
Ɗaya daga cikin 'yan uwansa na kusa ne ya tabbatar da rasuwar ranar Talata, 1 ga watan Agusta amma bai yi cikakken bayani ba.
Asali: Legit.ng