Cire Tallafin Man Fetur: MURIC Ta Nemi Tinubu Ya Bai Wa Musulmin Najeriya Bashi Mara Ruwa
- Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC), ta yi kira ga Shugaba Tinubu kan bai wa Musulmin Najeriya ba shi
- Kungiyar ta bukaci shugaban kasa da ya samar da tsari ta yadda Musulmin Najeriya za su rika samun rancen kudade marasa ruwa
- Daraktan kungiyar, Farfesa Ishaq Akintola ne ya yi kiran jim kadan bayan alkawuran bayar da bashi da Tinubun ya yi
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Kungiyar kare hakkin Musulmi (MURIC), ta nemi shugaban kasa Bola Tinubu da ya bayar da rancen kudade marasa ruwa ga Musulmin Najeriya.
Babban Daraktan MURIC, Farfesa Ishaq Akintola ne ya bayyana hakan a ranar Talata da ta gabata kamar yadda Legit.ng ta gano a shafin kungiyar.
Haramun ne Musulmi sun amshi bashi da ruwa
Akintola ya ce abinda ya sa MURIC ta nemi wannan bukata daga wajen Tinubu shi ne saboda haramun ne musulmi ya karbi ko ya ba da bashi da ruwa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Akintola ya ce MURIC ta yi wannan kiran ne saboda alkawuran da Tinubu ya yi lokacin da yake gabatar da jawabi ga 'yan kasa ranar Litinin.
A cikin jawabin nasa, Tinubu ya yi alkawarin bai wa 'yan kasa rancen kudade masu tarin yawa a kan ruwa dan kadan don rage musu radadin da cire tallafin man fetur ya jefa su ciki.
Akintola ya bayyana cewa, abinda shugaban ya yi abin a yaba ne, sai dai Musulmin Najeriya ba za su iya amfana da tsarin ba saboda tunanin lahirarsu.
Tsarin gudanar da mulki a Najeriya ya ci karo da tsarukan Musulunci
Akintola ya kuma koka cewa tsarin mulkin Najeriya, wanda turawan mulkin mallaka suka kakaba musu ya ci karo da tsarukan gudanar da rayuwa a Musulunci.
A dalilin haka ne Ishaq ya nemi Gwamnatin Tarayya da ta bullo da wasu tsarukan domin tabbatar da an yi wa Musulmai adalci, wanda yawansu ya kai akalla miliyan 130 a Najeriya.
"Idan Kana Sauraron Jawabin Tinubu, Za Ka Bukaci Fanka," Shehu Sani Ya Magantu Kan Jawabin Shugaban Kasa, An Yi Martani
Ya shawarci Tinubu kan ya tuntubi malaman addinin Musulunci musamman kan tsarukan da zai tanadar musu don gudun kawo rudani.
Sannan ya kuma ba da shawarar cewa a sanya kwararre kan harkokin kudi na Musulunci ya zama mamba a Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC).
Gwamnatin Tinubu za ta raba wa mutane sama da miliyan daya N50k kowanensu
Legit.ng a baya ta yi rahoto kan wani kudiri da da Shugaba Tinubu ya zo da shi na bai wa 'yan Najeriya sama da miliyan daya kyautar naira 50,000 kowanensu.
Timubu ya bayyana hakan ne ranar Litinin yayin da yake gabatar da jawabi na kai tsaye ga 'yan Najeriya.
Asali: Legit.ng