Mutane Sun Yi Sammako, ‘Yan Sanda Sun Fatattaki Masu Zanga-Zanga a Kano

Mutane Sun Yi Sammako, ‘Yan Sanda Sun Fatattaki Masu Zanga-Zanga a Kano

  • Mutane sun shiga zanga-zangar lumunar da aka fara domin yin Allah-wadai da tsare-tsaren gwamnati
  • A jihar Kano, masu yin zanga-zangar sun hallara tun sanyin safiyar yau, amma sun gamu da ‘yar cikas
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi kokarin ya lallashi mutane su hakura da zanga-zangar da aka shirya

Kano - A safiyar Talata, jami’an ‘yan sanda su ka fatattaki wasu cikin kungiyoyin da ke shirya zanga-zanga domin nunawa gwamnati fushinsu.

Daily Trust ta ce jama’a sun bi bayan kungiyar kwadago ta kasa (NLC), ana zanga-zanga da nufin nuna rashin amincewa kan janye tallafin fetur.

Wani wanda ya shaida abin da ke faruwa, ya ce an fara zanga-zangar kafin zuwan ‘yan sanda.

Zanga-Zangar ‘Wahalar Rayuwa’ a Kano
Jama'a su na kallon Gwamnan Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Tun karfe 7:00 na safe, masu zanga-zangan su ka taru a gidan Murtala, kusa da titin Kofar Nasarawa, tafiyar kilomita biyu zuwa karamar hukumar birni.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Majalisar Dattawa Ta Dauki Mataki Bayan Masu Zanga-Zanga Sun Kutsa Kai Cikin Harabarta Da Karfin Tuwo

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma lokacin da manema labarai su ka iso, sai ‘yan sanda su ka mamaye wurin da aka yi zanga-zangar.

‘Yan kwadago sun hurowa gwamnati wuta a dalilin tashin farashin man fetur. Zanga-zangar sun kankama a Legas, Benin, Benin Oyo da garin Abuja.

Legit.ng Hausa ta samu labari mutane sun taru a shatale-talen unguwar Mundubawa da ke garin na Kano domin fara wannan zanga-zangar lumuna a yau.

Kiran da Abba Gida-Gida ya yi

Mutane sun yi watsi da Gwamna, an fara zanga-zanga gadan-gadan a jihar Kano

A cewar Vanguard, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya roki kungiyar NLC ta hakura da yin wannan zanga-zanga, ya ce za a shawo kan lamarin.

Mai girma Abba Kabir Yusuf ya shaidawa ma’aikata cewa gwamnatoci a kowane mataki, su na kokarin kawo tsare-tsare domin rage wahalar da ake ciki.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari Ya Ya Ja Kunnen Gwamnatin Tinubu Kan Hambarar da Bazoum a Nijar

Sanusi Bature Dawakin-Tofa ya ce gwamnan Kano ya bayyana haka ne a wajen taron da ya yi da CRC a gidan gwamnati, yake cewa zai fito da tsare-tsare.

Daga cikin hanyoyin da gwamnati za ta bi domin saukakawa al’umma akwai dawo da motocin Kanawa da rabawa dalibai kayan makaranta a kyauta.

Tinubu a tsaka mai wuya

Idan kungiyar ECOWAS ta zura ido kan lamarin Nijar, rahoto ya zo cewa ‘yan ta’adda za su iya sake mamaye Najeriya yadda aka yi lokacin Boko Haram.

A gefe guda kuma amfani da karfi zai iya jawo kasashen Afrikan su shiga yaki, su yi ta kashe junansu yayin da manyan Duniya za su zura masu idanu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng