Kungiyar Kwadago Ta Dakatar Da Gudanar Da Zanga-Zanga? Gaskiya Ta Fito Fili
- Joe Ajaero, shugaban ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa babu gudu ba ja da baya dangane da zanga-zangar da ƙungiyar ta shirya
- Ajaero, a cikin wata sanarwa da ya rattaɓawa hannu. ya ce hukumar ba ta sake duba matsayarta ba ko dakatar da zanga-zangar da ta shirya gudanarwa ranar Laraba
- Tun da farko sakataren ƙungiyar na ƙasa, Emma Ugbaja, ya yi nuni da cewa ƙungiyar za ta gana da mambobinta domin sanin matakin da za ta ɗauka bayan zamanta da gwamnatin tarayya
Ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta yi fatali da rahotannin da ke cewa tana duba yiwuwar dakatar da zanga-zangar gama-gari da ta shirya gudanarwa a faɗin ƙasar nan, ranar Laraba, 2 ga watan Agustan 2023.
A wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a shafinta na Twitter da yammacin ranar Talata, 1 ga watan Agusta, ƙungiyar tace ba ta sake duba matsayarta ba ko dakatar da zanga-zangar kamar yadda aka rahoto tunda farko.
Babu batun fasa zanga-zanga, Joe Ajaero
A cewar sanarwar wacce shugaban ƙungiyar na ƙasa, Joe Ajaero ya rattaɓawa hannu, ƙungiyar ta haƙiƙance cewa har yanzu ba ta sauya zani ba kan buƙatun da ta ke neman a biya mata.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ƙungiyar ta haƙiƙance cewa za ta gudanar da zanga-zangar a gobe Laraba, kamar yadda ta shirya.
Emma Ugbaja, sakataren ƙungiyar ƙwadagon, bayan kammala zama da kwamitin gwamnatin tarayya, ya ce matakan da Shugaba Tinubu ya fara ɗauka abun a yaba ne amma sun yi kaɗan.
Daga nan ya yi nuni da cewa ƙungiyar ƙwadagon da ƙungiyar ma'aikata za su tattauna da mambobinsu domin cimma matsaya kan matakin da za su ɗauka zuwa ƙarshen ranar Talata kafin a fara zanga-zangar ranar Laraba.
NLC ta bayyana cewa ranar Laraba za a fara gudanar da zanga-zanga
Bayan Taro a Aso Villa, NLC Ta Yi Magana Kan Janye Zanga-Zanga da Shiga Yajin Aikin da Ta Shirya a Najeriya
Amma bayanan dake fitowa daga wajen Ajaero, sun nuna cewa matsayar ƙungiyar ba ta sauya ba dangane da zanga-zangar.
Wani ɓangare na sanarwar na cewa:
"Muna son mu sanar da ƴan Najeriya cewa mun kammala zama da gwamnatin tarayya, inda mu ka so mu sanya su saurari buƙatun al'umma da ma'aikatan Najeriya."
NLC Za Ta Tattauna Da Mambobinta
Da zu rahoto ya zo cewa ƙungiyar ƙwadago ta ƙasa (NLC) ta bayyana cewa za ta tattauna da mambobinta domin duba yiwuwar janye zanga-zanga.
Ƙungiyat ta bayyana hakan ne dai bayan ta kammala zama da wakilan raba tallafi na shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Legit.ng