Tallafin Mai: DSS Da Yan Sanda Ne Suka Janyo Hauhawar Farashin Man Fetur – Shugaban IPMAN
- Kungiyar IPMAN, ta bayyana cewa jami'an tsaro suna taka muhimmiyar rawa wajen tashin farashin man fetur
- Kungiyar ta ce karɓar kuɗaɗe na ba gaira ba dalili da jami'an DSS da na 'yan sanda ke yi ne ya ƙara janyo tsadar man
- Ya kuma alaƙanta tsadar da tashin farashin kuɗaɗen waje da kuma karyewar darajar naira
Abuja - Shugaban Kungiyar dillalan man fetur mai zaman kanta ta Najeriya (IPMAN), ya ce jami'an tsaro na farin kaya (DSS), da kuma jami'an 'yan sanda, sun taka muhimmiyar rawa wajen carkewar farashin man fetur.
Ya ce baya ga farashin man daga kasuwannin duniya, karbar kudaden da DSS da ‘yan sanda ke yi ne ya janyo ƙarin farashin man fetur na baya-bayan nan daga N537 zuwa N617 kamar yadda Vanguard ta wallafa.
Shugaban na IPMAN, Chinedu Okoronkwo ya bayyana hakan ne a yayin wani taro na jin ra'ayoyin jama'a da kwamitin binciken tsadar man na Majalisar Wakilai ya shirya ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
NNPCL ya riƙewa IPMAN naira biliyan 250
Chinedu ya kuma bayyana cewa babu isassun kuɗaɗe a hannun ƙungiyar dillalan man fetur ɗin saboda maƙalewa da kuɗaɗen na su suka yi.
Ya ce a yanzu haka IPMAN ta na bin kamfanin mai na Najeriya (NNPCL), bashin kuɗaɗe har naira biliyan 250, wanda hakan ya sa ba za su iya shigo da man fetur kai tsaye ba.
Ya kuma yi kira ga gwamnati da ta dakatar da hukumominta daga amsar haraji ba bisa ƙa'ida ba, domin yana daga cikin abubuwan da ke janyo tsadar man kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Yadda za a magance tsadar man fetur da ake fama da ita a Najeriya
Tsadar Mai: IPMAN Ta Koka, Ta Bayyana Yadda 'Yan Kasuwar Man Fetur Ke Ji a Jika a Dalilin Cire Tallafi
Da yake tsokaci kan yadda za a shawo kan matsalolin da ake fuskanta a harkokin mai, Chinedu ya ba da shawarar a koma amfani da iskar gas ta CNG.
Ya ce muddun za a koma amfani da CNG, to lallai za a magance matsalar tsadar man da ake fuskanta wacce ta samo asali daga cire tallafin da aka yi.
Duk da matsin da ake fama da shi, Chinedu ya ce wajibi ne Najeriya ta cire tallafin man fetur ɗin domin amfani da kuɗaɗen wajen gyara wasu ɓangarori na tattalin arziƙin ƙasa.
Ya kuma bayyana cewa karyewar darajar naira ma na taka muhimmiyar rawa wajen tashin farashin man da ake amfani da shi a Najeriya a rahoton na jaridar Vanguard.
Tinubu ya ce Najeriya tara sama da naira tiriliyan 1 daga cire tallafi
Legit.ng a baya ta yi rahoto iƙirarin da Shugaba Tinubu ya yi na cewa gwamnatinsa ta tara sama da naira tiriliyan ɗaya daga cire tallafin man fetur.
Yanzu-Yanzu: "Mun Tara Sama da N1tr" Shugaba Tinubu Ya Tona Kuɗin Da Ya Ƙwato Bayan Cire Tallafin Fetur
Ya bayyana hakan ne ranar Litinin, yayin da yake jawabi na kai tsaye ga 'yan Najeriya.
Asali: Legit.ng