Denmark Ta Kafa Dokar Da Za Ta Haramta Kona Qur'ani A Kasarta Baki Daya

Denmark Ta Kafa Dokar Da Za Ta Haramta Kona Qur'ani A Kasarta Baki Daya

  • Tun bayan kona Qur'ani mai girma a kasar Sweden, kasashe da dama ke daukar matakan kare faruwar hakan
  • Kasar Denmark ta bi sahu inda ta gabatar da dokar da za ta hana kona Qur'ani mai girma da sauran littattafan addini a kasar
  • Ministan harkokin wajen kasar, Lars Lokke shi ya tabbatar da haka inda ya ce abin takaici ne yadda ake cin zarafin Musulunci

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Gwamnatin kasar Denmark za ta zartar da dokar hana kona Qur'ani mai girma da sauran littattafan addini a kasar.

Denmark ta mika kudirin doka ga majilisar dokokin kasar don hana aikata hakan a ofisoshin jakadancin kasashe.

Denmark ta gabatar da dokar haramta kona Qur'ani a kasar
Kasar Denmark Da Sweden Na Duba Yiyuwar Haramta Zanga-zanga Da Kona Qur'ani A Kasashensu. Hoto: BBC.
Asali: UGC

Ministan harkokin wajen Denmark ya bayyana yadda dokar ta ke

Wannan na zuwa ne bayan wani matashi ya kona Qur'ani mai girma a bakin babban masallacin Juma'a na birnin Stockholm a Sweden, Aminiya ta tattaro.

Kara karanta wannan

Akpabio Ya Koka Kan Karancin Albashin 'Yan Majalisar Dattawa, Ya Ba Da Dalili

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Lars Lokke, ministan harkokin wajen kasar shi ya bayyana haka yayin ganawa da gidan talabijin na DR da ke kasar.

Ya ce kona Qur'ani mai girma tunzurawa ne da kuma cin zarafin mabiya addinin Musulunci, inda ya ce lokaci ya yi da za su dauki mataki, cewar BBC News.

Ya koka kan yadda aka kona Qur'ani a Sweden da asarar da hakan ta jawo

Ministan ya ba da misalin abin da ya faru a kasar Sweden a kwanakin baya da cewa ya lalata alakar diflomasiyya da kasashen Musulmi.

Ya ce yanke alakar ya jawo mata asara marar misaltuwa ta bangarori da dama a kasar.

Lokke ya ce firaministan kasar ya mika dokar ga majalisar, abin da suke jira shi ne amincewarsu akan tabbatar da dokar, Vanguard ta tattaro.

Sweden: Sarkin Musulmi Ya Yi Allah Wadai Da Kona Qur’ani, Ya Ce Hakan Cin Zarafi Ne

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Hanyoyi 4 na kare kai daga fadawa ta'addanci bayan cire tallafin man fetur

A wani labarin, Sarkin Musulmi, Abubakar Sa'ad ya yi Allah wadai da kona Qur'ani mai girma a kasar Sweden da aka yi a ranar babbar sallah.

Sultan ya ce wannan aika-aika cin zarafin addinin Musulunci ne da neman tsokana da kuma tunzura mabiya addinin.

Sultan ya koka kan yadda kasashen da suke ikirarin wayewa za su zuba ido ana cin zarafin Musulunci haka ba tare da daukar wani mataki ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.