Nuhu Ribaɗu Ya Gana da Gwamnonin Shiyyar Kudu Maso Gabas a Abuja

Nuhu Ribaɗu Ya Gana da Gwamnonin Shiyyar Kudu Maso Gabas a Abuja

  • Nuhu Ribadu, mai ba shugaba Tinubu shawara kan harkokin tsaro ya gana da gwamnonin shiyyar Kudu maso Gabas a Abuja
  • Ba bu wata sanarwa a hukumance kan maƙasudin wannan taro na sirri amma ana ganin ba zai rasa alaƙa da tabarbarewar tsaro ba
  • Majalisar dattawa ta fara ɗaukar matakan kawo karshen dokar zaman gida da IPOB ta ƙaƙaba a Kudu maso Gabas

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT Abuja - Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaron ƙasa, Malam Nuhu Ribaɗu ya yi ganawa cikin sirri da gwamnoni 5 na shirryar Kudu maso Gabashin Najeriya.

Har kawo yanzu ba bu cikakken bayanin kan muhimman batutuwan da suka tattauna a wannan ganawa da ta gudanar ranar Litinin, 31 ga watan Yuli, 2023 a Abuja.

NSA Nudu Ribadu.
Nuhu Ribaɗu Ya Gana da Gwamnonin Shiyyar Kudu Maso Gabas a Abuja Hoto: Nuhu Ribadu/Facebook
Asali: Facebook

Amma ana hasahen mai yiwuwa taron ba zai rasa nasaba da yadda matsalar tsaro ke kara tabarbarewa a jihohin Anambra, Enugu, Abiya, Imo da kuma Ebonyi ba.

Kara karanta wannan

Tinubu: Yadda Za a Raba Wa Mutum 1,300 Tallafin N50,000 a Kowace Ƙaramar Hukuma, Bayanai Sun Fito

Channels tv ta tattaro cewa a ranar Laraba da ta shige, majalisar dattawan Najeriya ta yi Allah wadai da dokar zaman gidan da yan ta'adda suka ƙaƙaɓa a Kudu maso Gabas.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar ta kuma nemi gwamnatin tarayya da ta hada kai da Gwamnatin Finland domin taso ƙeyar mai fafutukar kafa kasar Biafra, Simon Ekpa, zuwa Najeriya.

A cewar majalisar dattawan, ya kamata a dawo da ɗan fafutukar neman ɓalle wa daga Najeriya domin a gurfanar da shi a gaban Kotu doka ta yi aiki a kansa.

Majalisar dattawa ta fara ɗaukar matakin kawo karshen lamarin

Bugu da ƙari, majalisar dattawa ta cimma matsayar gayyatar ministan harkokin waje (idan aka naɗa shi) da sauran masu ruwa da tsaki domin gudanar da bincike.

Ta ce bayan binciken, za a gurfanar da duk wani mai ɗaukar nauyin ayyaukan ta'addanci a shiyyar gaban ƙuliya domin ya girbi abinda ya shuka, a cewar rahoton Vangaurd.

Kara karanta wannan

Kwanaki Kadan da Yin Juyin Mulki a Nijar, Bola Tinubu Ya Tafi Biki a Kasar Afrika

Sanatocin sun kuma yi fatali da buƙatar sakin jagoran ƙungiyar 'yan aware IPOB, Nnamdi Kanu, tana mai cewa hakan raina shari'a ne domin Kes din na gaban Kotu.

Majalisar Dattawa Ta Ɗauki Matsaya Kan Ministan da Ya Fara Firamare Yana Shekara 3

A wani rahoton kuma Ministan da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa daga jihar Benuwai ya haddasa ruɗani da kace-nace a majalisar dattawa.

Yayin tantance shi ranar Litinin, Farfesa Utsev ya faɗa wa majalisa cewa an haife shi a 1980 kuma ya fara karatun Firamare a 1984.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262