Yan Bindiya Sun Hallaka Masu Kai Kudin Fansa 2 A Jihar Plateau Bayan Karbar Kudaden
- 'Yan bindiga a jihar Plateau sun hallaka wasu matasa da suka kai kudin fansa don ceto ‘yan uwansu
- Wadanda aka kashen, Agada Sambo da Azi sun fito daga garin Angware da ke karamar hukumar Jos ta Gabas
- Mazaunin yankin, Sule Moses ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce an kashe matasan ne a ranar 29 ga watan Yuli
Jihar Plateau – ‘Yan bindiga sun hallaka mutane biyu bayan sun kai musu kudin fansa don karbo ‘yan uwansu a jihar Plateau.
Wadanda aka kashen sun fito ne daga garin Angware da ke karamar hukumar Jos ta Gabas da ke jihar.
Jaridar Punch ta bayyana wadanda suka rasa rayukan nasu da Agada Sambo da ke kauyen Zangam a garin Maigemu sai kuma wani da ake kira da Azi.
Wani mazaunin yankin Angware, Moses Sule ya tabbatar da kashe matasan a ranar Litinin 31 ga watan Yuli inda ya ce an kashe su a ranar Asabar 29 ga watan Yuli, Tribune ta tattaro.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
'Yan bindigan sun hallaka mutanen bayan kokarin kai musu kudin fansa
Sule ya ce an binne gawarwakinsu a ranar Lahadi 30 ga watan Yuli yayin da jami’an tsaro suka bazama neman ‘yan bindigan ruwa a jallo.
Ya ce:
“A nan yankin Angware, hedikwatar karamar hukumar Jos ta Gabas, ‘yan bindiga sun kashe wasu matasa biyu a daren ranar Asabar 29 ga watan Yuli.
“Wadanda aka kashen su ne Agada Sambo na kauyen Zangam a yankin Maigemu sai kuma Azi daga kauyen Kayarda da ke Maigemu duk a karamar hukumar Jos ta Gabas.
“Agada ya je zai biya kudin fansa don sakin wani mutum mai suna Luka Izang bayan sace shi da aka yi makwanni biyu da suka wuce.”
Ya bayyana yadda 'yan bindigan suka kashe mutanen biyu
Ya kara da cewa:
“’Yan bindigan sun saki Izang yayin da kuma suka rike Agada, wani mutum mai suna Jerry ya sake zuwa da kudin fansa don karbo Agada, sun karbi kudin inda suka kori Jerry tare da kashe Agada da Azi.
“Har yanzu ‘yan sanda da wasu ‘yan sa kai sun bazama cikin daji neman ‘yan bindigan a yankin Maigemu da ke karamar hukumar.”
Kokarin neman wayar kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Alabo Alfred ya ci tura yayin da wayarsa ta kasance a kashe, cewar Newstral.
Sojoji Sun Kama Shanu 1000 Da Ke Gararamba A Gonakin Jama’a Da Musu Barna
A wani labarin, rundunar soji a jihar Plateau sun kama shanu fiye da dubu daya a karamar hukumar Mangu.
Rundunar ta ce ta kama dabbobin ne bayan ganinsu suna gararamba a gonakin mutane tare da yi musu barna.
Ta ce za ta dauki matakin da ya dace tare da kama masu dabbobin idan suka zo neman dabbobinsu.
Asali: Legit.ng