Fintiri Ya Ce Zai Rushe Duk Gidan Da Aka Samu Dauke Da Kayan Abincin Da Aka Wawuso Daga Ma'ajiya
- Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya buƙaci waɗanda suka saci kayayyakin abinci su dawo da su
- Ya bayyana hakan ne a Yola biyo bayan wawushe kayayyakin abinci da aka yi daga rumbun ajiyar jihar
- Gwamnan ya ce za su bi gida-gida su duba, inda ya sha alwashin rushe duk gidan da aka samu ɗauke da kayan satar
Yola, jihar Adamawa - Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri ya ce suna shirye-shiryen raba kayayyakin tallafi duk da fasa ma'ajiyar abincin jihar da aka yi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wani taro na manema labarai da ya gudana a Yola babban birnin jihar kamar yadda The Cable ta wallafa.
An kama sama da mutane 100 kan satar kayayyakin abinci
A ranar Lahadi ne rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da kama sama da mutane 100 saboda satar kayayyakin abinci daga rumbun ajiyar gwamnatin jihar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Biyo bayan hakan ne gwamnan jihar ya sanya dokar taƙaita zirga-zirga, sannan kuma ya nemi al'ummar jihar da su bai wa jami'an tsaro goyon baya.
Da yake jawabin, gwamnan ya ce za su tabbatar da cewa tallafin abincin ya isa kowane gida da ke faɗin jihar duk da ta'adin da aka yi.
Gwamnan ya nemi mutane su dawo da kayayyakin da suka sata
Gwamna Fintiri ya umarci mutanen da suka saci kayayyakin abinci daga rumbun ajiyar, da su yi gaggawar miƙa abubuwan da suka sata zuwa ofishin 'yan sanda mafi kusa da su kafin ƙarfe 12 na ranar 1 ga watan Agusta.
Ya ce zai bayar da umarnin bi gida-gida domin gudanar da bincike, kuma duk gidan da aka samu da irin kayan satar, za a rushe shi.
Ya ce burinsu shi ne a raba kayayyakin kowa ya samu ba wai wasu su zo su kwashe su kaɗai ba.
Ga bidiyon jawaban da gwamnan ya gabatar a gidan gwamnati da ke Yola:
Nema ta tsaurara tsaro a rumbun ajiyar abinci na jihar Kaduna
Legit.ng a baya ta kawo rahoto kan matakin da hukumar ba da agajin gaggawa (NEMA), a jihar Kaduna ta ɗauka na tsaurara tsaro a rumbun ajiyar kayayyakin tallafinta da ke jihar.
Hakan ya biyo bayan fasa ma'ajiyar kayayyakin tallafi da mutane suka yi a jihar Adamawa.
Asali: Legit.ng