Karin Albashi, Kayan Abinci, Motocin Gas Da Albishir 6 Da Bola Tinubu Ya Yi Yau
- Bola Ahmed Tinubu ya yi jawabi a matsayinsa na shugaban Najeriya a kan halin da kasa ta ke ciki
- Gwamnatin tarayya za ta batar da Naira Biliyan 125 domin a taimakawa masu kananan kasuwanci
- Za a taimakawa manoma da masu bukatar motocin hawa a sakamakon janye tsarin tallafin fetur
Abuja - Mai girma Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da jawabi ga al’umma da karfe 7:00 na yammacin ranar Litinin, watanni biyu da shigansa ofis.
Jawabin shugaban Najeriyan ya maida hankali ne game da tattalin arziki da manufofin da gwamnatinsa za ta kawo domin a iya rage radadi.
Za mu kashe N75bn a kan masana’antu 75, kowane daga cikin masana’antun nan zai iya samun N1bn domin su bunkasa karfin masana’antarsu.
Kamfanoni da SME
Gwamnatin tarayya za ta kashe biliyoyin ne tsakanin Yulin 2023 da Maris na 2023. Za a biya bashi ne a cikin shekaru biyar dauke da ruwa na 9%.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Za mu kashe N50bn ga kasuwanci miliyan daya daga yanzu zuwa Maris 2024. Manufarmu ita ce bada N50, 000 ga ‘yan kasuwa 1, 300 a jihohi.
Tinubu a jawabinsa ya ce zai kashe N125bn domin tallafawa kananan kasuwanci 100. Masu neman jari za su samu bashin da za a biya a shekaru hudu.
Noma da rabon kayan abinci
Gwamnati mai-ci ta bada umarnin fitar da metric ton 200, 000 na hatsi daga rumbun kasa. Sannan za a raba metric ton 250, 000 na takin zamani a jihohi 36.
Gwamnatinmu za ta batar da N50bn domin a shuka shinkafa da masara a eka 150, 000. Za kuma a ware N50bn domin shuka alkama da rogo a Najeriya.
Bayan cire tallafin fetur
Akwai motoci da za a raba a jihohin kasar nan da za su biya nan da watanni 60 a kan ribar 9%.
Mun kuma yi tanadin kashe N100bn tsakanin yanzu zuwa watan Maris 2024 domin sayo motoci 3000 masu daukar mutane 20 masu amfani da gas.
Bayan samun damar adana N1tr bayan cire tallafin fetur, shugaban kasan ya sanar da za ayi wa ma’aikata karin albashi da zarar an gama tattaunawa.
Nadin Ministocin tarayya
Adeseye Ogunlewe ya taba zama Minista a gwamnatin PDP, kuma tsohon Sanata ne, an ji labarin ya bayani a kan ministocin da za a nada a kasar nan.
‘Dan siyasar ya nuna akwai wasu da Sanatoci za su tantance a saukake, kuma akwai wadanda sai an fafata kafin a amince su rike kujerar Minista.
Asali: Legit.ng