An Kuma, Yan Ta'addan Boko Haram Sun Yi Wa Manoma Yankan Rago a Borno

An Kuma, Yan Ta'addan Boko Haram Sun Yi Wa Manoma Yankan Rago a Borno

  • Mayakan Boko Haram sun sake yi wa manoma kusan 10 yankan rago a jihar Borno da ke Arewa maso Gabashin Najeriya
  • Wata majiya daga mazauna yankin ta bayyana cewa yan ta'addan sun bi manoman har gonakinsu sannan suka yanka su
  • Jami'an tsaro ne suka shiga gaba yayin da mazauna kauyen da abun ya shafa suka je ɗauko gawar manoman

Borno state - Wasu da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne sun yi wa manoma kusan 10 yankan rago a gonakinsu a garin Kawuri, karamar hukumar Konduga a jihar Borno.

Majiyoyi daga mazauna yankin da jami'an tsaro sun shaida wa wakilin Daily Trust cewa lamarin ya faru ne a ranar Litinin da misalin karfe 8:15 na safe.

Mayakan Boko Haram.
An Kuma, Yan Ta'addan Boko Haram Sun Yi Wa Manoma Yankan Rago a Borno Hoto: dailytrust
Asali: Getty Images

Wannan harin na zuwa ne ‘yan makonni ƙalilan bayan ‘yan ta’addan sun kashe manoma kusan 15 a kananan hukumomin Damboa da Jere na jihar da ke Arewa maso Gabas.

Kara karanta wannan

Innalillah: 'Yan bindiga sun kashe babban malamin Izala da wasu 5 a jihar Kaduna

Yadda wannan sabon harin ya rutsa da manoma 10

A cewar wani magidanci mai suna Malam Muhammad Sherif, maharan sun bi sawun manoman kuma suka halaka su a gonakinsu da ke kusa da kauyen Dam Alu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Manoman na cikin aiki a gonakinsu, sai ‘yan ta’addan suka far musu kuma suka yanka masu makogwaro. Yanzu haka muna shirya gawarwakinsu domin yi musu jana'iza nan ba da dadewa ba."
“Kisan manoma ya zama ruwan dare a nan a garuruwan Kawuri da Alau. Sun kashe mutane biyu a yau, jiya an kashe mutum uku. Hakan ya sake jefa damuwa a zuƙatanmu," in ji shi.

Shin babu jami'an tsaro ne a yankin?

Da aka tambaye shi ko babu jami’an tsaro a yankin, sai ya ce, “Sojoji ba su da nisa da garin, kuma manoman sai sun yi tafiya mai nisa kafin su isa gonakinsu."

Kara karanta wannan

Arewa Na Digan Jini Yayin Da 'Yan Bindiga Suka Yi Garkuwa Da Mata 23 Da Ma'aikatan Kamfani 10 a Zamfara

“Masu tayar da kayar bayan sun yi ta zagaya wa a kusa da Dam Alau da kuma dazukan kewaye. Galibin manoman da ake kashewa wadanda suka ki basu haɗin kai ne."

Daya daga cikin majiyoyin jami’an tsaron da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaida cewa sun jagoranci mazauna garin wajen kwato gawarwakin manoma 10 domin a musu jana'iza, rahoton Guardian ya tabbatar.

Yan Sanda Sun Kama Sama da Mutum 100 da Ake Zargi da Aikata Laifuka a Bauchi

A.wani rahoton kuma Jami'an yan sandan jihar Bauchi sun samu nasarar damƙe waɗanda ake zargi da aikata muggan laifuka sama da 100.

Kwamishinan 'yan sandan jihar, Auwal Muhammad, ya ce jami'ai sun kwato makamai masu haɗari daga hannun mutanen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262