Tinubu Ya Gargadi Makarantun Gaba Da Sakandare Akan Karin Kudaden Makaranta
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gargadi makarantun gaba da sakandare kan kare-karen kudade a makarantu babu dalili
- Mai ba wa shugaban shawara akan harkar sadarwa, Dele Alake shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa a yau Litinin 31 ga watan Yuli
- Tinubu ya amince da cire duk wasu matakai da ka iya kawo cikas ga dalibai wurin karbar lamuni, hakan zai ba wa dalibai damar cin gajiyar bashin
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gargadi makarantun gaba da sakandare kan kare-karen kudade babu dalili.
Dele Alake, mai ba wa shugaban shawara akan harkar sadarwa shi ya bayyana haka a yau Litinin 31 ga watan Yuli, cewar TheCable.
Shugaba Tinubu ya kuma amince da cire duk wasu takunkumi da za su hana dalibai samun damar lamunin kudade da shugaban ya ware na dalibai.
Ya ce hakan ne kadai zai ba wa ko wane dalibi damar samun lamunin ba tare da wata matsala ba, cewar Tori News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya cire takunkumi a ba da lamunin daliban
A cewar sanarwar:
“Don tabbatar da ko wane dalibi ya ci gajiyar lamunin ba tare da watsar da karatu saboda rashin kudi ba da kuma tsadar rayuwa, Tinubu ya amince da cire duk wasu ka’aidoji na lamunin.
“Ya yi hakan ne don ba wa dukkan dalibai daman samun lamunin kudin cikin sauki ba tare da samun cikas ba.”
“Har ila yau, Tinubu ya gargadi makarantun gaba da sakandare da su guji kare-karen kudade babu gaira babu dalili sabanin kudin makaranta da ake biya saboda a kada iyaye da dalibai su takura.
Tinubu ya ware Ton fiye da 200,000 na abinci don rabawa mutane
Sanarwar ta kara da cewa:
“Yayin da Tinubu ya umarci ware fiye da Tan 200,000 na tsabar abinci ga mutanen Najeriya da birnin Tarayya Abuja.
“Gwamnatin Tarayya ta na jinjinawa daliban Najeriya kan irin kokarin da suka yi duk da irin halin da ake ciki na matsin tattalin arziki.
“Shugaba Tinubu ya himmatu wurin ba wa harkar ilimi muhimmanci da samar da abubuwan more rayuwa wa dalibai da kuma inganta harkar koyarwa na malamai a kasar.”
Tinubu Zai Samar Da Motocin Bas Ga Dalibai, Ya Cire Musu Takunkumin Lamunin Karatu
A wani labarin, Shugaba Bola Tinubu ya amince da samar wa dalibai bas don jigilarsu.
Shugaban ya kuma cire takunkumin lamunin karatu ga daliban don ba wa kowa damar samun lamunin cikin sauki.
Asali: Legit.ng