Shehu Ya Bayyana Dalilai 13 Da Bai Kamata Najeriya Ta Mamayi Jamhuriyar Niijar Ba

Shehu Ya Bayyana Dalilai 13 Da Bai Kamata Najeriya Ta Mamayi Jamhuriyar Niijar Ba

Shehu Sani, Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, ya zayyano wasu manyan dalilai 13 da ya ce bai kamata 'yan Najeriya su goyi bayan yakar sojojin jamhuriyar Nijar da ake shirin yi ba.

Ya bayyana hakan ne a wani dogon rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Litinin, 31 ga watan Yuli.

Shehu Sani ya shawarci Najeriya kar ta shiga faɗa da jamhuriyar Nijar
Shehu Sani ya zayyano dalilai 13 da bai kamata Najeriya ta yarda ta yaƙi Nijar ba. Hoto: Shehu Sani, Hot In Juba
Asali: Facebook

Shehu Sani ya shawarci Tinubu ya tsame hannunsa, ya bar 'yan Nijar su kwatarwa kansu 'yanci

Shehu Sani ya shawarci Tinubu da kar ya bari a zuga shi ya mamayi Nijar, inda ya kuma shawarce shi da ya ƙyale 'yan ƙasar su kwatowa kawunansu 'yanci.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Idan za a iya tunawa, Kungiyar Raya Tattalin Kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), sun bai wa sojojin na Nijar wa'adin kwanaki bakwai su maida mulki hannun hamɓararren shugaban ƙasar Muhammed Bazoum.

Kara karanta wannan

Ta Rikice a Nijar, Masu Zanga-Zanga Sun Farmaki Ofishin Jakadancin Faransa

Hakan ya biyo bayan ayyana kansa da shugaban masu tsaron shugaban ƙasar Abdourahamane Tchiani ya yi a matsayin sabon shugaban Nijar a ranar juma'a da ta gabata.

Dalilai 13 da Shehu Sani ya bayyana kan rashin dacewar yakar sojojin Nijar da ECOWAS ke shirin yi

Da yake mayar da martani kan matakin da ECOWAS ta ɗauka dangane da juyin mulkin na Nijar, Shehu Sani ya zayyano wasu ƙwararan dalilai 13 da yake ganin ya kamata a duba su kamar haka:

1. Mamayar Nijar da ECOWAS za ta yi daidai yake da yaki tsakanin Najeriya da Nijar saboda kusancin da kasashen biyu suke da shi.

2. Ƙasar Rasha da dakarun Wagner May ka iya shigowa domin kawowa Nijar ɗauki, inda Shehu ya ce dole ne kuma a yi amfani da kuɗaɗen Najeriya wajen yin yaƙin.

3. Yaƙin zai shafi jihohin da ke kan iyaka irin su Sokoto, Zamfara, Katsina, Jigawa da Yobe.

Kara karanta wannan

Akwai sharrin Turawa: Shehu Sani ya fadi abubuwa 5 da suke sa juyin mulki a Afrika

4. Ba a yaƙi sojojin ƙasashen Guinea, Mali, Burkina Faso da Chad ba a lokacin da suka kwace mulki a kasashensu.

5. Sojojin Amurka da na Faransa da ke cikin jamhuriyar Nijar ba su dakatar da juyin mulkin ba.

6. Nijar ta kasance ta na taimakawa Najeriya na tsawon shekaru, kuma yanzu haka akwai sama da 'yan gudun hijira 303 na Najeriya da ke zaune a can.

7. Duka ƙasashen Afrika za su tarawa Najeriya nauyi da zarar an fara yaƙin.

8. Shehu Sani ya shawarci Tinubu ya ƙyale 'yan Nijar su ƙwatarwa kansu 'yanci.

9. Ya ba da misali da ƙasar Saudiyya wacce ya ce har yanzu ba ta gama farfaɗowa ba saboda maƙudan kuɗaɗen da ta kashe a yaƙin Yemen.

10. Shehu ya kuma ba da misali da ƙasar Myanmar, wacce har yanzu babu wata ƙasa da ta yi yunƙurin ɗaukar mataki a kanta duk da tana hannun sojoji

Kara karanta wannan

Dubu Ta Cika: An Kama Ƙasurgumin Ɗan Bindiga da Yaransa 4 da Suka Addabi Mutane a Jihohin Arewa 2

11. Ya ce akwai yaƙi dan 'yan ta'adda da har yanzu Najeriya ke fama da shi da ya kamata ta kammala.

12. Ya ce Mali, Burkina Faso da Guinea ka iya shigowa domin taimakawa Nijar.

13. Shehu Sani ya shawarci Shugaba Tinubu da ya ci gaba da zama teburin sulhu da sojojin da suka amshe mulki a Nijar.

Dole Bazoum ya koma mulki, Amurka ta goyi bayan ECOWAS

Legit.ng a baya ta kawo muku cewa ƙasar Amurka ta goyi bayan ƙungiyar ƙasashen ECOWAS, wajen ganin an mayar da mulki hannun Bazoum.

Amurka ta ce ba za ta yarda da mulkin jamhuriyar Nijar ba a hannun soja saɓanin farar hula ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng