Gwamna Ya Haramta Wa Basarake Sayar Da Filaye a Jihar Osun

Gwamna Ya Haramta Wa Basarake Sayar Da Filaye a Jihar Osun

  • Gwamnatin jihar Osun ta haramtawa wani basarake shiga duk wasu harkoki na hada-hadar filayen a jihar
  • An zargi basaraken mai suna Abeeb Agbaje da cinye gonakin mutanen da yake jagoranta
  • Gwamnatin jihar ta bayyana cewa munanan ayyukan da basaraken ke yi ya taɓa ƙimar gwamnatin jihar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Osun - Gwamnatin jihar Osun ta haramta wa wani basarake a IleOgbo, mai suna Oba Abeeb Agbaje harkokin sayar da filaye a masarautarsa biyo bayan korafe-korafen da aka shigar a kansa.

An dakatar da shi ne daga shiga duk wata hada-hada ta filaye da kuma amfani da makusantansa wajen yin karfa-ƙarfa da kwace filayen ‘yan kasa.

Hakan ta faru ne a ranar Larabar da ta gabata, a lokacin da ya gurfana gaban kwamishinan shari’a na jihar Jimi Bada da kuma na ƙananan hukumomi da masarautu, Dosu Babatunde, biyo bayan korafin da mutane suka shigar a kansa.

Kara karanta wannan

ECOWAS Ta Bayyana Matakin Da Za Ta Dauka Kan Sojojin Da Suka Kifar Da Mulki a Nijar

An dakatar da basarake daga tsoma baki kan harkokin filayen a yankinsa
Gwamnan Osun ya haramta wa basarake shiga hada-hadar filayen a yankinsa. Hoto: Sulaiman Uwaisu Idris
Asali: Facebook

An shigar da ƙorafe-ƙorafe a kan basaraken

Kwamishinan ya ce an shigar da ƙorafe-ƙorafe da dama a kan basaraken dangane da abubuwan da suka shafi ƙwacen filaye da barazana ga mutanen yankin kamar yadda Premium Times ta wallafa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya ƙara da cewa matakin ya zama dole ne don dakatar da basaraken daga zaluntar mutanen yankin da yake jagoranta kan haƙƙoƙinsu.

Babatunde ya kuma ƙara da cewa ba iya mutanen ƙauyen na IleOgbo ne suka kawo ƙorafi kan basaraken ba, ya ce akwai 'yan ƙauyukan da ke maƙwabtaka da su da suka shigar da ƙorafi a kansa ta hanyar amfani da dogaransa da kuma 'yan sanda.

Basaraken na ɓatawa gwamnatin jihar suna

Kwamishinan ya kuma ce an kuma umarci Mista Agbaje da ya gargaɗi ɗaya daga cikin dogaransa mai suna Gbadewolu Kasali, da sauransu daga tsoma baki kan harkokin sayar da filaye a yankin kamar yadda The Guardian ta wallafa.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An Tafka Gagarumar Asara Bayan Gobara Ta Lakume Rukunin Wasu Shaguna a Jihar Arewa

Ya kuma bayyana cewa munanan ayyukan da basaraken ya daɗe yana aiwatarwa suna taɓa martabar gwamnatin jihar.

Ya ƙara da cewa abubuwan da basaraken yake yi ya sanya wasu mutanen sun fa zargin cewa da gwamnatin jihar ake haɗa baki ana ƙwace musu filaye.

Sannan ya ce gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti da zai gudanar da bincike kan lamarin, gami da mayarwa waɗanda aka zalunta haƙƙoƙinsu.

Tinubu ya nemi muhimmiyar buƙata daga sarakunan gargajiya

Legit.ng a baya ta yi wani rahoto kan ganawar da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi da sarakunan gargajiya.

A zaman da suka yi ranar 9 ga watan Yuni, Tinubu ya buƙaci sarakunan gargajiyan da su goyi bayan manufofinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng