Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Zai Yi Jawabi Ga 'Yan Najeriya a Yau Litinin

Da Dumi-Dumi: Shugaba Tinubu Zai Yi Jawabi Ga 'Yan Najeriya a Yau Litinin

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da jawabi ga ƴan Najeriya a ranar Litinin da misalin ƙarfe 7:00 na dare
  • Shugaban ƙasar zai gabatar da jawabin ne ga ƴan Najeriya domin yin ƙarin haske kan shirye-shiryen da gwamnatinsa take yi
  • Jawabin na shugaban ƙasar na zuwa ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke ci gaba da kuka kan tsadar rayuwa da ake fama da ita ƙasa

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da jawabi ga ƴan Najeriya ranar Litinin, 31 ga watan Yuli da misalin ƙarfe 7:00 na dare.

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Dele Alake, shi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Litinin da safe, cewar rahoton Daily Trust.

Shugaba Tinubu zai yi jawabi ga 'yan Najeriya
Tinubu zai gabatar da jawabi ga 'yan Najeriya ranar Litinin da yamma Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter
Gidajen talbijin, gidajen rediyo da sauran kafafen watsa labarai su kama gidan talbijin na Nigerian Television Authority (NTA) da gidan rediyon Radio Nigeria domin haska jawabin." A cewar sanarwar

Kara karanta wannan

"Shugaba Tinubu Ba Zai Yi Dana Sanin Nada Ni Minista Ba", Jawabin Wike Yayin Tantance Shi a Majalisa

Babu cikakken bayani akan abinda shugaban ƙasar zai yi jawabi a kansa ba, sai dai jawabin na sa na zuwa ne a lokacin da ƴan Najeriya ke ci gaba da ƙorafi kan tsadar rayuwa a dalilin tsige tallafin man fetur da gwamnatinsa ta yi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ƴan Najeriya na cikin raɗaɗi

Ƴan Najeriya na kuka kan raɗadin da ake ciki a ƙasa a sakamakon tsadar kayan masarufi wacce ta samo asali a dalilin tsige tallafin man fetur.

Shugaban ƙasar ya sha yin kira ga ƴan Najeriya inda yake cewa gwamnatinsa na aiki tuƙuru domin ganin cewa ƴan Najeriya sun samu ingantacciyar rayuwa.

Shugaba Tinubu ya yi nuni da cewa raɗaɗin da ake sha a ƙasar nan na ɗan wucin gadi ne, inda ya bayyana cewa nan ba da daɗewa ba ƴan Najeriya za su dara.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Gwamnan Jihar Arewa Ya Sanya Dokar Kulle a Jiharsa, Ya Bayyana Kwakkwaran Dalili

Jawabin na sa yana zuwa ne ana dab da tsunduma zanga-zangar gama-gari wanda ƙungiyar ƙwadago ke shirin farawa, da yajin aikin da ƙungiyar manyan likitoci take yi, bayan ta yi fatali da ƙarin kaso 25% na albashi da gwamnatin tarayya ta yi musu.

Fastoci Sun Gargadi Tinubu Kan Cire Tallafi

A wani labarin kuma, gamayyar fastocin majami'a sun nuna damuwarsu kan yadda cire tallafin man fetur ke neman durƙusar da ƙasar nan.

Kungiyar ta bayyana cewa rashin tsari mai kyau na rage radadin cire tallafi ba karamin hatsari ba ne ga kasar baki daya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng