Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Yi Magana Bayan Hoton Sanusi II Ya Dawo Gidan Gwamnati

Gwamnatin Abba Gida-Gida Ta Yi Magana Bayan Hoton Sanusi II Ya Dawo Gidan Gwamnati

  • An daura hotunan Muhammadu Sanusi II da na Shugaban kasa da Gwamna a gidan Gwamnatin jihar Kano
  • Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta tunbuke Sanusi II daga sarautar gidan dabo bayan an yi zaben 2019
  • Ana rade-radin Basaraken zai sake rike sarautar gidan dabo idan har Jam'iyyar NNPP ta kafa gwamnati a Kano

Kano - Legit.ng Hausa ta fahimci an hangi hotunan Sarkin Kano na 14, Mai martaba Muhammadu Sanusi II a gidan gwamnatin jihar Kano.

Wani ‘dan kasuwa mai suna Kabiru Garba ya daura wannan hoto a shafin Facebook a ranar Lahadi.

Injiniya Kabiru Garba da ya fito da abin sarari ya kyankyasa cewa Muhammadu Sanusi II zai dawo kan karagar mulkin da ya bari a 2019.

Muhammadu Sanusi II
Muhammadu Sanusi II da yaronsa Ashraf Hoto: @Adam_L_Sanusi
Asali: Twitter
“Idan mun gayawa Mutane su rika karyata mu, wannan ma so min tabi ne. Yana nan zuwa, ku jira.”

Kara karanta wannan

Binani, Keyamo, Fashola Da 'Yan Siyasa 10 Da Ba Su Da Rabon Zama Ministoci

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

- Kabiru Garba

A bidiyon da wani Imran Muhammad ya wallafa a dandalin Twitter, za a iya ganin ana gyare-gyaren dakin rantsuwar da ke Kano.

Martanin Ashraf Sanusi da sauran jama'a a

"Wannan ya zama jan-kunnen karshe ga makiyan Muhammad Sanusi II. Dubi yadda abubuwa za su kare, ba sa'anku ba ne."

- Ashraf Sanusi

Habun Zee Mai Waka ya ce:

“Dawowar Sarki. Mun gode Gwamna Abba Kabir Yusuf”

Ameer Abdullahi Adam ya rubuta:

“Aiki ya yi kyau, In shaa Allahu yana kan hanya.”
“Dole a Saka Hotonsa Saboda Nadin Sarautarsa Aka Gina Wajen Shine Tarihin.”

- Yahaya Sani Adam

Habib Khalid Na'ibi ya ce ba haka abin yake ba; “Wannan ai Hall din gidan makama ne.”

“Sai ma ranar da za mu je taro shi in Shaa Allah” Inji wani Bawan Allah.

Kara karanta wannan

Bayan Shekaru 8, Abba Gida Gida Zai Karasa Aikin da Kwankwaso Ya Bari a Kano

"Ganin hoton nan kadai ya sani farin ciki. Allah ya tabbatar da alkhairi"

-Khalil Kabir Turaki

Gwamnatin Abba tayi karin haske

Gwamnatin Kano ta yi karin haske game da abin da ya jawo aka ga hoton Khalifa Muhammadu Sanusi II a dakin rantsuwa na gidan gwamnati.

Salisu Hotoro wanda yana cikin masu taimakawa Gwamna Abba Kabir Yusuf a kafofin sadarwa na zamani, ya ce Sanusi II ya shiga littafin tarihi.

Ko ba komai, hadimin gwamnan na Kano ya ce ana girmama Sarki na 14, ganin hotonsa bai nufin wani abin na daban kamar yadda ake tunani.

Karin bayanin Gwamnati

"Sarki Muhammad Sanusi II shi ne mutum na farko a cikin jerin sarakunan Kano da ya karbi sandar girma a babban dakin taro na 'Coronation' da ke fadar gwamnatin jihar Kano.
Matukar ana so a girmama tarihi dole ne a saka hoton sa a wannan dakin taro, ganin hoton Sarki Muhammad Sunusi II a Coronation hall bai kamata ya zama sabon wani darasi na tattaunawa ba domin kuwa ko a yanzu ka shiga gidan gwamnatin jihar Kano zaka ga hotunan dukkanin mutanen da suka taba mulkar Kano kuma suka zauna a fadar gwamnatin jiha, saka wannan hotuna kuma ba yana nufin wani abu bane face girmama tarihi.

Kara karanta wannan

Kwankwaso, Ganduje Da Mutane 3 Da Ake Ganin Tinubu Zai Iya Bai Wa Mukamin Minista Daga Kano

Allah ya taimaki jihar mu ta Kano, Allah ka shiga lamarin Kanawan Dabo."

- Salisu Yahaya Hotoro

Nadin Ministoci ya kai dare

A baya, an samu labari Bola Tinubu ya rasa yadda zai yi rabon kujerar Ministan Kano tsakanin Kwankwasawa masu mulki a yau da ‘Yan Gandujiyya.

Akwai inda Tinubu ya zabi Ministansa, amma ‘yan jihar su ka nuna ba su amince da wanda za a kawo ba, a Kano har yanzu ba a yanke shawara ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng