Jam’iyyar PDP Za Ta Dauki, Jama’a a Kafar Sada Zumunta Sun Yi Ma Ta Wankin Babban Bargo
- Wasu ‘yan Najeriya sun mayar da martani kan sanarwar da jam’iyyar PDP ta fitar na daukar wani muhimmin aiki
- Jam'iyyar PDP ta sanar da cewa za ta dauki ma'aikacin da zai yi aiki a matsayin Darakta Janar na People Democractic Institute (PDI)
- Matakin dai ya janyo cece-ku-ce daga ‘yan Najeriya, wadanda suka bayyana shi a matsayin sabon abu kuma mai daukar hankali
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jam’iyyar PDP ta sanar da daukar ma’aikacin da zai mata aiki a matsayin Darakta Janar na People Democractic Institute (PDI).
Sanarwar ta fito ne ta shafinta na @OfficialPDPNig a kafar X Corp a ranar Lahadi, 30 ga watan Yuli.
Duk wanda ke da sha’awar yin aikin, an ce dole ya zama yana da digiri na biyu a fannin ilimin zamantakewa kuma ya kasance kwararre mai gogewar akalla shekaru 6.
MaIi son cika fom din neman aikin zai iya tura takardunsa ga ofishin jam’iyyar da ke Wadata Plaza a Wuse, Abuja.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
‘Yan Najeriya sun yi martani
Wani ma’abocin amfani da manhajar X Corp, The Legit Kanayor @kanaior, ya ce ya kamata PDP ta dauki Shugaban Matasansu ya yi aiki, ya ce:
"Ya kamata dai ku zama masu yin abu da gaske don Allah...Kuna iya daukar Shugaban Matasanku mai Babbar riga domin ya samu abin yi.."
Wani dan Najeriya, Ibrahim Garba @Garbaibrahim1, bai ji dadin yadda wai sai dai a tura takardan neman aikin zuwa ofishin PDP ba.
"Ya kamata ku zama jam’iyyar zamani mana, yanzu fa karni na 21 ne, ba ku da bukatun aika sako ba ku da Imel ne?
Wani idooh Charles @charles_idemoh, ya rubuta:
"Zan iya ba ku ambulan mai tsoka don samun wannan?”
TheCitizen @Alex_Obe10, ya bayyana matakin a matsayin mai kyau daga babbar jam'iyyar adawa.
"Babban ci gaba ne. Fatan karin daukaka ga babbar jam'iyyarmu"
Don Hinvest Global @HinvestGlobal, ya dauki batun daukar aikin a matsayin alamar rudewar PDP.
“PDP ta rude.”
Tinubu ya nada fitaccen masani don yin bincike a lamurran CBN
A wani labarin, shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu na Najeriya ya nada wani jami’in bincike na musamman da zai binciki Babban Bankin Najeriya (CBN) da wasu hukumomi masu alaka da shi.
A wata wasika da majiya ta gani, shugaban ya bayyana Jim Osayande Obazee, babban jami’in Hukumar ba da Rahoton Kudi ta Najeriya (FRCN), a matsayin mai binciken.
Shugaban kasar ya bukaci mai binciken na musamman da ya binciki CBN da manyan Kamfanonin Kasuwancin Gwamnati (GBEs).
Asali: Legit.ng