Jam’iyyar NNPP Ta Rusa Shugabancinta Na Jihohi Bakwai Saboda Gangarowar Rashin Da’an Cikin Gida

Jam’iyyar NNPP Ta Rusa Shugabancinta Na Jihohi Bakwai Saboda Gangarowar Rashin Da’an Cikin Gida

  • Yayin da aka kusa zaben gwamna a wasu jihohi, an bayyana rusa shugabancin jam’iyyar NNPP ta su Kwankwaso
  • Wannan na faruwa ne bayan da aka gano wasu daidaiku na cin dunduniyar jam’iyyar ba gaira babu dalili
  • Ya zuwa yanzu, jam’iyyar ta bayyana matsayarta da kuma matakin da ta ke dauka kan wadanda aka dakatar

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

FCT, Abuja ¬Jam’iyyar NNPP ta rusa daukacin shugabanninta tun daga gundumomi har zuwa jiha a jihohi bakwai na tarayyar kasar nan saboda abubuwan da suka faru na cin dunduniyar jam’iyyar.

Jihohin da abin ya shafa sun hada da Enugu da Ekiti da Ribas da Neja da Katsina da Kaduna da kuma Zamfara, The Guardian ta ruwaito.

Haka kuma jam’iyyar ta dakatar da dan takararta na gwamna a zaben da ya gabata a jihar Enugu, Cajetan Eze da dan takarar sanata na Enugu ta Arewa, Farfesa Onyeka A. Onyeka.

Kara karanta wannan

Ganduje Ya Gamu da Cikas, Wasu Kusoshin APC Sun Faɗa Wa Tinubu Wanda Ya Cancanci Zama Shugaban APC Na Gaba

Yadda aka rushe shugabancin NNPP
NNPP ta rushe shugabancinta a wasu jihohi | Hoto: tribuneonlineng.com
Asali: UGC

Gaskiyar abin da ya faru

Wannan na fitowa ne daga bakin sakataren yada labarai na jam’iyyar, Dr. Agbo Major yayin da yake zantawa da magana da manema labarai bayan taron kwamitin ayyuka na kasa na jam’iyyar a ranar Juma’a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya kara da cewa, jam’iyyar ta kuma dakatar da ayyuka game da shugabancin jam’iyyar a jihar Imo saboda zaben gwamna da ke tafe a jihar nan kusa.

Ya ce matakin rusa shugabannin jam’iyyar a jihohin daban-daban ya biyo bayan korafe-korafen ‘ya’yanta ne a jihohin da rahoton kwamitin ladabtarwa da ya bincika a kwanan nan.

Dalilin rusa shugabancin NNPP

Ya ce an samu yawaitar samun matsalolin cin dunduniyar jam’iyyar a jihohin da abin ya faru, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

A cewarsa, an kafa kwamitin riko mai mutum biyar ga jihohin da abin ya shafa ba tare da bata lokaci ba don yin bincike.

Kara karanta wannan

Ko Ganduje Zai Zama Shugaba? Jam'iyyar APC Ta Sanaya Ranakun Manyan Tarukanta 2

Kwamitin na ayyuka ya kara da cewa, ya da umarnin a gaggauta cike dukkan guraben da ba kowa a jihar Imo kamar yadda kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya tanada.

Jigon NNPP a Kano ya karyata labarin samun mukami a tarayya

A wani labarin na daban, Abdulmumin Jibrin ya fito karara ya musanya maganar cewa an ba shi kujerar Ministan tarayya a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

A wani matukar takaitaccen bayani da ya yi a shafin Facebook, Hon. Abdulmumin Jibrin ya nuna jita-jitar da ake yadawa sam ba gaskiya ba ce.

Jibril mai wakiltar Kiru/Bebeji a majalisar wakilan tarayya ya nuna labarin karya ne yake yawo, ko da dai bai yi wani bayanin abin da yake nufi ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.