Tsadar Kudin Mai: Kayan Abinci 4 Mafi Tsada a Gwamnatin Tinubu
Legas - Cire tallafin man fetur ya janyo tashin farashin man da ya yi sanadiyyar carkewar farashin kayayyakin amfani na yau da kullum a kasuwannin Najeriya.
Kayayyakin abinci ma ba a barsu a baya ba, domin kuwa suma sun yi tashin gwauron zabi wanda hakan ya janyo ƙarancin cinikinsu.
Halin da ake ciki a kasuwar jihar Legas
Wakiliyar Legit.ng ta tattauna da 'yan kasuwa da dama a Legas, inda suka shaida mata halin da ake ciki.
Wasu daga cikinsu sun koka kan ƙarancin kayayyakin da suke sayarwa saboda yanayin lokacin da ake ciki, yayin da wasu kuma suka koka kan yadda tsarukan Shugaba Tinubu suka shafi kasuwancinsu.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Kayayyakin abinci 4 mafi tsada a kasuwar Legas a wannan watan na Yuli
A binciken da Legit.ng ta gabatar a shahararriyar kasuwar Legas, ta tattaro muku kayayyakin abinci 4 da suka fi tsada a halin da ake ciki.
1. Shinkafa
A yanzu haka a Legas, buhun shinkafar da ake sayarwa a kan naira 35,000, ya tashi zuwa dubu 41,000.
Ana samun ƙaramin buhu na shinkafa 'yar cikin gida, duk da tsakkuwa da ake samu a cikinta akan naira 35,000.
2. Ogbono
Wani ɗan kasuwa da ya daɗe a harkar kasuwancin kayayyakin abinci, ya shaidawa Legit.ng cewa ana sayar da buhun Ogbono sabon zuwa a kan naira 120,000, yayin da ake sayar da tsohon zuwa naira 200,000 zuwa 210,000.
Ogbono wani abu ne da ake amfani da shi wajen yin miyar da ake cin tuwo, akpu da teba da shi.
3. Egusi
Buhun egusi ya yi tashin gwauron zabi a manyan kasuwannin da ke cikin jihar Legas.
Bankin Duniya Ta Fitar Da Jerin Kasashe 10 Da Suka Fi Fuskantar Hauhawan Farashin Abinci, Babu Najeriya Cikinsu
A yanzu haka a kasuwar Mile 12 da ke Legas, ana sayar da buhun egusi kan naira 180,000, a wasu shagunan ma yakan kai naira 190,000 zuwa abinda ya yi sama.
Wannan shi ne farashin da 'yan sari ke sayo shi a mafi yawan wurare a kasuwannin na Legas.
4. Tumatiri
Tumatiri ma dai na daga cikin kayayyakin masarufin da ke cin karensa babu babbaka a kasuwannin jihar Legas
Ana sayar da kwandon lafiyayyen tumatiri a kan naira 40,000 zuwa 50,000 yayin da ake sayar da kwandon bagen tumatirin akan naira 25,000 zuwa ƙasa.
Tsadar tumatir dai ba ta rasa nasaba da yanayi na damina da ake ciki, inda farashinsa yake sauka sosai a lokacin kakarsa.
Ba iya abubuwa huɗu da muka zayyano ba ne suka yi tsada a kasuwannin Najeriya, sai dai tsadar da suka yi, wacce ta wuce tunanin mai tunani ne ya sa muka mayar da hankali a kansu.
Matasa Sun Kutsa Katafaren Rumbun Ajiyar Kayayyaki Na Ɗan Majalisa, Sun Tafka Ta'adi, An Rasa Rayuka a Arewa
Gwamnan jihar Adamawa ya ragewa ma'aikata 'yan fansho raɗadi
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto cewa gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri, ya amince da bai wa ma'aikata da 'yan fansho a jihar tallafin naira 10,000.
Gwamnan ya yi hakan ne domin rage musu raɗaɗin cire tallafin man fetur da ya jefa 'yan ƙasa da dama cikin halin ha'ula'i.
Asali: Legit.ng