Jihohin Borno, Yobe Da Adamawa Sun Daukewa Dalibai Da Ma'aikata Wahalhalun Sufuri Bayan Cire Tallafi
- Jihohin Adamawa da Yobe da kuma Borno sun samar da wasu hanyoyi da za su ragewa mutane radadin cire tallafi
- A jihar Borno, gwamnati ta samar motoci da ke jigilar mutane a cikin gari a farashi mai rahusa
- Yayin da jihohin Yobe da Adamawa suka shirya tsaf don daukewa mutane wahalhalu dalilin cire tallafin mai
Jihar Borno - Gwamnatocin jihohin Borno da Yobe da Adamawa sun fara samar da hanyoyin ragewa jama'a radadin cire tallafin mai.
Gwamnatocin jihohin uku sun rage kudin sufuri musamman a tashoshin mota mallakinsu don rage radadin da ake ciki.
A jihar Borno, Gwamna Babagana Zulum ya amince da kara motoci 50 don rage wahalar da mutane ke ciki, Daily Nigerian ta tattaro.
Yadda jihar Borno ta ragewa al'ummarta radadi
Mai ba wa gwamnan shawara akan harkokin yada labarai, Isa Gusau ya ce sun kara bas 50 ne a tashar motar Borno Express don kawo sauki.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Gusau ya kara da cewa gwamnatin ta samar da wasu motoci na diban kaya 30 don taimakawa manoma, Peoples Gazette ta ruwaito.
Wani dalibi a jami'ar Maiduguri, Mustapha Abdullahi da wani ma'aikaci Ali Modu sun yabawa gwamnatin jihar inda suka ce sun hau motocin yayin da suka biya N50 kacal.
Abdullahi ya ce:
"Na hau motar Borno Express a N50 daga Post Office zuwa jami'ar Maiduguri madadin N150 da muke biya a baya."
Jihohin Adamawa da Yobe sun bi sahun Borno don samar da sauki
A jihar Adamawa, gwamnati ta kafa kwamit na musamman don rage radadin cire tallafi.
Shugaban kwamitin, Amos Edgar ya ce gwamnatin ta shirya siyar bas bas don rage tsadar sufuri a cikin gari, cewar Premium Times.
Darakta a ma'aikatar sufuri, Labaran Salisu ya ce za su mayar da motoci 250 na ma'aikatar don zirga-zirga a cikin gari a farashi mai rahusa.
A jihar Yobe kuwa, sakataren Hukumar Agaji a jihar, Mohammed Goje ya ce gwamnatin jihar ta shirya tsaf don samar da motocin sufuri kyauta ga ma'aikata da dalibai.
Ya ce:
"Nan ba da jimawa ba gwamnatin jihar za ta samar da bas bas don zirga-zirgar dalibai da ma'aikata kyauta."
Cire Tallafi: Kwamitin Rabon Kayan Tallafi na Tinubu Ya Fitar Da Sabbin Bayanai
A wani labarin, Kwamitin da shugaban kasa, Bola Tinubu ya kafa don raban kayan tallafi sun gudanar taro a Abuja.
Rahotanni sun tabbatar cewa gwamnonin jihohin Bauchi da Anambra da Benue da Kaduna sun samu halartar taron.
Yayin da a wani bangare, wakilan Kungiyar Kwadago ta kasa (NLC) suma na daga cikin wadanda suka halarci taron.
Asali: Legit.ng