Akwai Tasirin China da Rasha a Yawaitar Juyin Mulkin Kasashen Yammacin Afrika, Inji Shehu Sani
- Bayan juyin mulkin Nijar, mutane da yawa na ci gaba da bayyana martani da kuma ra’ayoyinsu kan tushen lamarin
- Sanata Shehu Sani ya ta’allaka juyin mulkin da yawaitar damawa da ‘yan China da Rasha, da kuma yawaitar talauci
- Idan baku manta ba, sojoji sun hambarar da mulkin farar hula a jamhuriyar Nijar, lamarin da ya jawo cece-kuce
Najeriya - Wani tsohon dan majalisa a majalisar dattawan Najeriya, Sanata Shehu Sani, ya mayar da martani kan mamayar da sojoji suka yi a fadar shugaban kasan Jamhuriyar Nijar.
A ranar Laraba, 26 ga watan Yuli, aka tabbatar da yin juyin mulki a jamhuriyar Nijar, inda aka hambarar da gwamnatin farar hula ta Mohamed Bazoum
Rahotanni sun ce an kama shugaba Bazoum tare da tsare shi bayan wata mamaya da sojojin tawaye suka yi a fadar shugaban kasa da ke Yamai, babban birnin kasar.
Ganduje Ya Gamu da Cikas, Wasu Kusoshin APC Sun Faɗa Wa Tinubu Wanda Ya Cancanci Zama Shugaban APC Na Gaba
Martanin Shehu Sani
A nasa martanin a kafar X Corp a ranar Asabar, 29 ga watan Yuli, Sanata Shehu Sani ya bayyana dalilai da dama da je yiwa dimokuradiyya barazana kana ya baje ta kasa a yankin Yammacin Afirka.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya bayyana cewa juyin mulkin da sojoji ke yi a kasashen Yammacin Afirka ya samo asali ne sakamakon lalacewar damawa jama'a da kuma daura dimokradiyya kan jirgin tangal-tangal da ‘yan siyasa ke yi.
Sanata Sani ya yi nuni da cewa tabarbarewar tattalin arziki a yankin ya rikide zuwa matsanancin talauci, wanda hakan ya jawo tsagwaron yunwa da fatara da rashin tsaro.
A rubutunsa, cewa ya yi:
“Ina ganin akwai abubuwa guda biyar da suka haddasa rugujewar gwamnatocin dimokaradiyya a Yammacin Afirka da yanzu ke haifar da juyin mulkin soja.
Kace-Nace Yayin Da 'Yan Najeriya Suka Soki Yadda Tinubu Ya Zabi Ministoci, Sun Bayyana Abin Da Ya Kamata
"1. Rikita tsarin dimokuradiyya da 'yan siyasa suka yi da kuma dagula rayuwar jama’a.
'2. Kalubalen tattalin arziki da ke haifar da yaduwar talauci da yunwa.
"3. kalubalen tsaro; yaduwar kungiyoyin ta'addanci da tsananin dogaro da sojoji.
"4. Habakar tasirin Rasha da China a fannin tattalin arziki, tsaro da siyasa.
"5. Rashin kakaba takunkumin mai tasiri kuma mai ma'ana kan masu juyin mulki."
Ya kuma kara da cewa, karuwar tasirin da kasashen China da Rasha ke yi a wannan yanki shi ne babban makasudin yawaitar juyin mulkin.
Sojoji sun sanar da hambarar da Bazoum a juyin mulkin Nijar
A tun farko kunji cewa, an cire Mohammed Bazoum daga kan karagar mulki a Nijar ta hanyar wani danyen juyin mulki da aka gudanar a ranar Larabar nan.
Rahoton da mu ka samu daga Reuters ya tabbatar da cewa wasu sojoji sun yi wa gwamnati tawage sun kifar da Shugaba Mohammed Bazoum.
Bazoum Na Niger Ya Bayyana Matakin Da Zai Dauka Bayan Sojoji Sun Kifar Da Gamnatinsa, Minista Ya Yi Bayani
A wata sanarwa da su ka fitar ta bakin Kanal Amadou Abdramane, sojojin sun sanar da cewa sun kawo karshen gwamnati mai-ci a kasar Nijar.
Asali: Legit.ng