Iyalin Da Kowa Mai Facin Tayoyi Ne Harda Uba, Uwa Da Dansu, Bidiyonsu a Bakin Aiki Ya Yadu
- Wani bidiyo mai tsuma zukata na iyalin da ke sana'ar facin tayoyi domin daukar dawainiyar kansu na yau da kullun ya taba mutane da dama a soshiyal midiya
- Wata kwastama da ta kai motarta don ayi mata facin taya ta gano cewa ma'auratan da dansu mai shekaru 7 duk a shagon suke aiki
- Matar ta yi bayanin cewa ta bar aikinta don taimakawa mijinta kasancewar albashinta na wata baya isa wajen tallafawa iyalin
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wani bidiyo mai taba zuciya ya nuno gwagwarmaya da juriyar wani iyali wadanda ke gudanar da shagon facin tayoyi tare da dansu mai shekaru 7.
Bidiyon ya nuno wata mata wacce ta ziyarci shagon don gyara tayar motarta da ta samu faci.
Ta cika da mamaki ganin cewa wasu ma'aurata da dansu mai shekaru 7 ne suke gudanar da shagon, inda gaba daya suke aiki tukuru domin yi wa kwastamominsu aiki mai inganci.
Matar ta tambayi matar mutumin dalilin da yasa ita da danta suke aiki a shagon maimakon zama a gida ko mayar da hankali ga karatu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sai matar ta yi bayani cewa da tana aiki a matsayin malamar makaranta, amma albashinta na wata baya isa wajen daukar dawainiyar iyalin.
Ta ajiye aikinta sannan ta koma aiki tare da mijinta a shagon, inda za su samu karin kudi ta hanyar yin aiki tare.
Labarin iyalin ya taba matar sannan ta jinjina masu kan karfin gwiwa da jajircewarsu.
Bidiyon ya yadu a soshiyal midiya inda mutane da dama suna nuna sha'awarsu da tausayawa iyalin.
Kalli bidiyon a kasa:
Jama'a sun yi martani
@AkoredeOlawale373 ya yi martani:
"Wow, jinjina gareki, mata mai digiri tana taimakon mijinta a shago, Allah ya albarkaci iyalin."
@wuraolaashake ta ce:
"Wannan karamin yaron, Oh Allah...Ina sonka dana. Allah madaukakin sarki ya kasance tare da kai."
@Greatness64848 ta rubuta:
"Turancinta fes-fes Amincin Allah zai kasance tare da iyalin."
@oluwafisayomirepe ta yi martani:
"Wadannan mutanen na bukatar a karfafa masu gwiwa."
Bidiyon karamin yaro yana dinki a kan keke ya ja hankali
A wani labarin kuma, wani karamin yaro ya burge masu amfani da soshiyal midiya saboda kwarewarsa a dinki bayan shafin @stec_clothing0 ta wallafa bidiyonsa a TikTok.
A bidiyon, an gano yaron yana dinki cike da kwarewa a kan wani keken dinki mallakin mahaifiyarsa, wacce ta kasance tela.
Asali: Legit.ng