An Sace Rigar Daura Aure Ta Amarya a Cunkoson Ababen Hawa

An Sace Rigar Daura Aure Ta Amarya a Cunkoson Ababen Hawa

  • Wata amarya da ake dab da ɗaura mata aure ta gamu da 'yan fashi a cunkuson ababen hawa sun ɗauke mata rigar aure
  • Jennine Naidoo ta ce suna kan hanya ita da mahaifinta zasu je wurin Tela, ba zato wani matashi ya sace rigar
  • A cewarta, ta hakura da rigar a halin yanzu kuma ba ta kai rahoton lamarin ga yan sanda ba

Wata amarya mai jiran gado, Jennine Naidoo ta cika da mamaki bayan da ‘yan fashi suka sace mata rigar aurenta a cikin cunkoson jama’a.

A wani sako da ta wallafa a shafinta na sada zumunta, Naidoo ta ce ita da mahaifinta suna cikin mota zuwa wurin tela don canza rigar, lokacin da lamarin ya faru a ƙasar Afirka ta Kudu.

Amaryar da aka sace wa rigar aure a Afirka ta kudu.
An Sace Rigar Daura Aure Ta Amarya a Cunkoson Ababen Hawa Hoto: Jennine Naidoo
Asali: Facebook

Ta bayyana lokacin da aka kwace rigar daga bayan motarsu a cikin Durban CBD a ranar Litinin da safiya, farkon wannan makon

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Bar Iyayenta Don Rayuwa Da Saurayi a Daji, Bidiyon Ya Haddasa Cece-Kuce

Naidoo, wacce za a ɗaura mata aure a mako mai zuwa ranar Asabar, ta ce ta jima da sayen rigar a shirye-shiryen zuwan ranar Aurenta.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda lamarin ya faru

A kalamnta, Amaryar ta ce:

“Muna cikin tafiya a titin 'West Street' kusa da kasuwar China da ta ƙone lokacin da aka yi mana fashi. Lokacin da muka shiga cunkuson, mahaifina ya riƙa kallon madubin baya sabida mun san wurin ana fashi."
“Ba zato ba tsammani mahaifina ya lura da wani saurayi ya bude bayan abun hawarmu, sai muka fara ihu amma ya riga ya ciro rigar. Mun haɗa ido da wanda suke tare, har yana mun murmushi."
"Tun bara na sayi rigar kuma na yi farin ciki lokacin da na sanya ta. Amma ba zan taɓa son ta dawo hannu na ba. Duk da ta kasance ta musamman yanzu ina jin an gurbata ta."

Kara karanta wannan

Assha: Wata Amarya Ta Datse Mazaƙutar Angonta Kan Abu 1 a Jihar Katsina

Sai dai ta ce ba ta kai rahoton abinda da ya faru ga hukumar ‘yan sanda ba.

Me Zamu Jira? Magidanci Ya Maida Martani Ga Likitin da Ya Ce Kar Ya Kusanci Matarsa

A wani labarin kuma Wani mutumi ya shiga ƙunci bayan Likita ya shawarce shi da matarsa kar su kusanci juna na tsawon kwanaki 7.

Bayan kammala yi wa ma'auratan tsarin taƙaita iyali, Likita ya faɗa musu su ɗan yi hakuri da juna na tsawon mako guda domin aikin ya yi yadda ya kamata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262