Abba Gida Gida Ya Bude Cibiyoyin Koyar Da Sana'o'i Da Ganduje Ya Rufe a Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin bude cibiyoyin koyan sana'o'i 26 da Ganduje ya rufe
- Kwamishinan ayyuka da gidaje a jihar, Marwan Ahmad shi ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a Kano
- Ya ce tsohon gwamnan jihar, Rabiu Kwankwaso ne ya kirkiri cibiyoyin kafin tsohon gwamna Ganduje ya yi watsi da su
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya sanar da bude masana'antu 26 da tsohon gwamna Ganduje ya rufe a lokacin mulkinsa.
Kwamishinan ayyuka da gidaje a jihar, Marwan Ahmad shi ya bayyana haka ga manema labarai a ranar Alhamis 27 ga watan Yuli a Kano.
Umarnin Abba Kabir akan bude cibiyoyin
Ya ce tsohon gwamna, Rabiu Kwankwaso ne ya kirkiri cibiyoyin don koyawa matasa da mata sana'o'i, Daily Nigerian ta tattaro.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya kara da cewa Gwamna Abba Kabir shi ya ba da umarnin bude cibiyoyin ba tare da ba ta lokaci ba, cewar Pulse.
A cewarsa:
"Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci bude masana'antun da Rabiu Kwankwaso ya kirkira wanda gwamnatin da ta shude ta yi watsi da su.
"Cibiyoyin sun hada da: Koyan aikin jarida da harkan noma da kiyon kaji da koyon tuki."
Ya bayyana irin sana'o'in da ake koyarwa a cibiyoyin
Kwamishinan ya ci gaba da cewa:
"Sauran sana'o'n sun hada da yawon bude ido da wasanni da kuma harkar tsaro da sauransu."
Ya ce cibiyoyin za su ci gaba da aiki ne don samarwa matasa abin yi da dakile shaye-shaye da kuma ta'addanci da ta addabi mutanen jihar, cewar Vanguard.
Kwamishinan ya kuma kara da cewa gwamnatin jihar ta ci gaba da aikin ruwa na Jakara a cikin birnin Kano.
Gwamna Abba Gida Gida Na Kano Ya Biyawa Dalibai 55,000 Kudin Jarrabawar NECO
A wani labarin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya biyawa daliban jihar kudaden jarabawar hukumar NECO.
Gwamnan ya biya wa akalla dalibai 55,000 kudin jarabawar don inganta iliminsu a jihar ba tare da nuna wariya ba.
Abba ya gargadi daliban da su yi karatu tare da samun sakamako mai kyau don iyayensu da gwamatin jihar su yi alfahari da su.
Asali: Legit.ng