Akume Da Wasu Fitattun Yan Najeriya Da Ke Da Mata Da ‘Ya’ya a Majalisar Dokokin Tarayya
Akalla mata, 'ya'ya da kannen fitattun yan Najeriya shida ne suka samu shiga jerin yan majalisar dokokin tarayya 400 da aka rantsar a majalisar dokokin kasa ta 10 a ranar 13 ga watan Yunin 2023.
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wadannan yan majalisa mata sun yadu ne a majalisar dattawa da ta wakilai, inda suke wakiltan mazabu da yankuna daban-daban a jihohinsu.
Bisa rahoton jaridar Business Day, ga jerin sunayen mata, 'ya'ya da kannen yan siyasa da suka samu shiga majalisar tarayya ta 10 a kasa.
- Regina Akume
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Regina ta kasance matar babban sakataren gwamnatin tarayya, George Akume.
Sakataren gwamnatin tarayyan ya kasance gwamnan jihar Benue tsakanin 1999 da 2007.
An zabi Regina a karkashin inuwar jam'iyyar All Progressive Congress (APC) kuma tana wakiltan mazabar Gboko/Tarka na jihar Benue a majalisar wakilai.
An haifi Akume a shekarar 1955.
- Erhiatake Ibori-Suenu
Ta kasance diyar tsohon gwamnan jihar Delta, James Ibori.
Matar mai shekaru 42 tana wakiltan mazabar Ethiope East/Ethiope ta yamma a jihar Delta a majalisar wakilai.
An zabi Ibori-Suenu a matsayi mamba a majaliwar wakilai karkashin inuwar jam'iyyar PDP.
- Beni Butmak Lar Plateau
Ta kasance diyar marigayi Solomon Lar, mamba wanda aka kafa jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) da shi.
Tana wakiltan mazabar Langtang North/Langtang ta kudu a jihar Plateau kuma ta kasance yar jam'iyyar PDP.
An sake zabar Beni karo na biyar a majalisa a 2023 kuma ta zama yar majalisa ce a 2007.
An haifeta a ranar 12 ga watan Agustan 1967.
- Boma Goodhead
Tana wakiltan mazabar Akuku-Toru/Asari-Toru a jihar Ribas kuma ta kasance kanwa a wajen tsohon dan tawayen Niger Delta, Asari Dokubo.
An zabi Boma a karkashin inuwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
An haifi yar majalisar a ranar 24 ga watan Nuwamban 1970.
Ta shahara kan kalubalantar jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) wadanda suka tare kofar shiga harabar majalisar a shekarar 2018, inda suka hana ‘yan majalisa, ma’aikata, ‘yan jarida da sauran jama’a shiga harabar majalisar.
- Khadija Bukar Abba-Ibrahim
Ta kasance yar majalisa a karo na hudu, tana wakiltan mazabar Damaturu/Gujba/Gulani/Tarmuwa a jihar Yobe, rahoton Daily Trust.
Ta kasance matar tsohon gwamnan jihar Yobe Bukar Abba-Ibrahim.
Tsohuwar karamar ministar harkokin wajen ta kayar da dan mijinta wajen lashe tikitin APC.
An haifi yar majalisar tarayyar a ranar 6 ga watan Janairun 1967.
- Ireti Heebah Kingibe
An zabeta a matsayin sanata mai wakiltan babban birnin tarayya karkashin inuwar jam'iyyar Labour Party.
Ireti ta auri tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF) Babagana Kingibe.
Ta kasance kanwa a wajen Ajoke Mohammed, matar tsohon shugaban kasar Najeriya Murtala Mohammed.
An haifeta a ranar 2 ga watan Yunin 1954 (Shekaru 69).
Jerin matan da suka samu shiga majalisar dokokin tarayya ta 10
A gefe guda, Legit.ng ta rahoto cewa ba a cimma fafutukar da ake yi na ganin an samu daidaiton jinsi a majalisar dokokin tarayya ba, bayan rantsar da majalisar dokoki ta 10 a watan Yuni domin su fara ayyukan da aka zabe su a kai.
Yayin da kira ga samun karin mata yan majalisa ke kara yawa, adadinsu ya ragu idan aka kwatanta da majalisar dokoki ta tara.
Asali: Legit.ng