Jihar Niger: An Gano Jaririn da Wata Mata Ta Sace a Kasuwa a Bola
- Rahotanni sun bayyana cewa an gano jaririn da aka ɗauke a kasuwar Kure da ke Minna a jihar Neja
- Mahaifin jaririn ya ce an gano shi a cikin bola kusa da caji ofis ɗin 'yan sanda na Gauraka da ke ƙaramar hukumar Tafa
- Hukumar yan sanda ta ce bayan likitoci sun tabbatar da jaririn na cikin ƙoshin lafiya, an miƙa shi ga iyalansa
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Niger State - An gano wani jariri ɗan wata shida mai suna Chinedu Chukwueke, wanda aka sace a shagon mahaifiyarsa da ke Kasuwar Kure Ultra Modern Market, Minna, babban birnin jihar Neja.
Rahoton jaridar Daily Trust ya tattaro cewa mahaifin yaron, Mista Chikezie Stanley Chuks, shi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, 26 ga watan Yuli, 2023.
Ya ce an jefar da jaririn ne a wani juji da ke kusa da ofishin ‘yan sanda na Gauraka a karamar hukumar Tafa a jihar Neja, Arewa ta tsakiya a Najeriya.
Idan baku manta ba, rahoto ya nuna cewa wata mata ce ta ɗauke jaririn daga shagon mahaifiyarsa bayan ta yaudari mahaifiyar cewa tana son ta koyi gyaran gashi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
A wane hali aka gano jaririn?
Mahaifin yaron ya ce:
"An ga jaririn, matar ta jefar da shi a wani juji da ke kusa da ofishin ‘yan sanda na Gauraka kuma yana cikin koshin lafiya"
Yayin da aka tuntuɓe shi, jami'in hulɗa da jama'a na rundunar 'yan sanda reshen jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, ya tabbatar da gano jaririn wanda ya ɓata a kasuwa.
Kakakin 'yan sandan ya ce an ga jaririn ranar Laraba da misalin ƙarfe 12:30 na tsakar rana. A kalamansa, DSP Abiodun ya ce:
"Sakamakon matsin lamba da aka yi da kuma sanya ido sosai, an gano jaririn a wani ramin zaizayar kasa, kusa da makarantar firamare ta Gauraka da ke unguwar Gauraka a karamar hukumar Tafa.”
Wane mataki hukumar 'yan sanda ta ɗauka?
Ya ce an garzaya da jaririn zuwa asibiti mafi kusa don duba lafiyarsa, kuma likitoci sun tabbatar yana cikin koshin lafiya, daga nan kuma aka miƙa shi ga iyayensa.
Ya ce jami'an 'yan sanda na ci gaba da kokarin cafke matar da ta aikata wannan ɗanyen aikin domin fuskantar fushin doka, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Majalisar Dattawa Ta Amince Da Naɗe-Naɗen Tinubu 10 da Suka Shafi Arewa
A wani labarin Majalisar dattawa ta amince da buƙatar shugaba Tinubu ta naɗa mutane 10 a matsayin shugabannin hukumar raya Arewa maso Gabas.
Waɗanda Sanatocin suka amince da naɗinsu sun haɗa da ɗan ajin su tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, Janar Paul Tarfa daga Adamawa.
Asali: Legit.ng