Dan Najeriya Ya Fasa Ihu Yayin da Ya Kutsa Kai Sansanin Sojin Sama, Ya Roki Sojoji Su Bindige Shi

Dan Najeriya Ya Fasa Ihu Yayin da Ya Kutsa Kai Sansanin Sojin Sama, Ya Roki Sojoji Su Bindige Shi

  • An sha yar dirama a wani sansanin sojin sama yayin da dan farin huka ya gabatarwa sojoji bukata mai ban mamaki
  • Da yake magana cikin ihu, mutumin ya umurci sojoji da su harbe shi, cewa yana so ya tafi barzahu
  • Jama'a sun yi martani a kan bidiyon inda wasu da dama suka jinjinawa sojojin kan yadda suka tafiyar da abun cikin kwarewa

Wani mutumi da ba a bayyana sunansa ba ya haddasa cece-kuce a sansanin sojoji yayin da ya bukaci sojoji da su bindige shi.

A bidiyon da ya yadu a soshiyal midiya, mutumin ya daga hannunsa na dama sama sannan ya dungi ihun 'Allah', cewa shi yana so a harbe shi don ya tafi barzahu.

Matashi ya nemi sojoji su bindige shi
Dan Najeriya Ya Fasa Ihu Yayin da Ya Kutsa Kai Sansanin Sojin Sama, Ya Roki Sojoji Su Bindige Shi Hoto: @king_stoner
Asali: TikTok

Sojojin sun shiga rudani da wannan bukata tasa sannan suka bukace shi da ya bar wajen, amma mutumin ya ki sannan ya yarda da wani a kasa da ya kira shi da mahaukaci.

Kara karanta wannan

Rundunar Soji Ta Bayyana Ainihin Dalilin Kama Sojan Da Ya Bar Musulunci Ya Koma Kiristanci

Ya kalubalance su da su harbe shi, yana mai cewa shi ba zai bar wajen ba har sai an bindige shi. Sojojin ba su bi ta kan bukatarsa ba sannan suka yi kokarin raba shi da wajen.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Allah, ina son tafiya barzahu. Ku harbe ni, Ina son tafiya barzahu," inji mutumin.

Ganin cewa ba a biya masa bukatar tasa na rashin hankali ba, sai ya yi wa sojojin ba'a.

"Ba za ku ma iya harbi ba," cewarsa yayin da yake shirin barin harabar wajen.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Emmayoger ya ce:

"Shin wannan rundunar sojin Najeriya ne saboda ban taba ganin sojan Najeriya mai dattako kamar wannan ba."

fkgold ta ce:

"Lol "ba za ku ma iya harbina ba" shine ya fi bani dariya wannan ya fi mahaukaci yana neman mai kai shi kushewa."

Kara karanta wannan

A Kurarren Lokaci, Tinubu Ya Cire Mutum 4 a Jerin Wadanda Za A Ba Kujerar Minista

stallionguf ya ce:

"Mai gayen nan ya sha kafin ya isa wajen, na san cewa colos baya bayar da irin wannan karfin."

@RMH ta ce:

"Karon farko da na ga sojoji ba su yi wa mutumin da ya kalubalance su a bakin aikinsu duka ba.

ajimokomichael ya ce:

"Sojan ya nuna dattako da kawarewar aiki, ka ci gaba da gashi. gaba dai rundunar soji."

Yan Najeriya sun mato a kan babur mai cin mutum 7 da ke aiki da lantarki

A wani labari na daban, mun ji cewa wani bidiyon TikTok mai ban mamaki ya ja hankalin masu kallo da dama, yayin da yake dauke da kujerun zama na mutum bakwai kuma yana aiki ne da lantarki.

An gano wasu matasa biyu a kansa. Alamu ya nuna matasan na jin dadin rayuwarsu yayin da suke tuka babur din a titi, an shirya kujerun mutum bakwai bi da bi a tsakanin babur din.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng