'Yan Bindiga Sun Farmaki Tawagar Motocin Wani Kwamishina a Jihar Abia

'Yan Bindiga Sun Farmaki Tawagar Motocin Wani Kwamishina a Jihar Abia

  • Ƴan bindiga sun kai farmaki kan tawagar motocin kwamishinan kasuwanci da masana'antu na jihar Abia a birnin Aba
  • Ƴan bindigan sun farmaki kwamban motocin kwamishinan ne lokacin da yake tsaka da rangadin aiki a cikin birnin
  • Jami'an ƴan sanda biyu sun rasa rayukansu a mummunan harin, sannan ƴan bindigan sun kuma cinnawa ɗaya daga cikin motocin wuta

Jihar Abia - Ƴan bindiga sun farmaki kwamban motocin kwamishinan kasuwanci da masana'antu na jihar Abia lokacin da yake rangadi a cikin birnin Aba na jihar.

Harin wanda ya auku a ranar Talata da misalin ƙarfe 4:00 na yamma ya yi sanadiyyar rasuwar jami'an ƴan sanda biyu da ƙona wata motar gwamnati, cewar rahoton Channels tv.

Yan bindiga sun farmaki kwamishinan jihar Abia
'Yan bindigan sun farmaki kwamishinan ne lokacin da yake rangadi Hoto: Channelstv.com
Asali: UGC

Kwamban motocin kwamishinan dai suna kan hanyar zuwa babban shagon siyayya na Ekoha ne domin rangadin sabo da juna lokacin da ƴan bindigan suka buɗe musu wuta.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Sace Tsohon Shugaban Babbar Kwalejin Ilmi a Najeriya

A fafatawar da ta biyo baya, wani kurtun ɗan sanda dake tare da kwamban motocin ya mutu, yayin da wani jami'in ɗan sanda wanda yake a wajen domin wani abu daban shi ma ya rasa ransa.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bayan asarar rayukan da aka yi, ƴan bindigan sun kuma ƙona mota ɗaya ta ma'aikatar kasuwanci da masana'antu, rahoton Sahara Reporters ya tabbatar.

Rundunar ƴan sandan jihar ta yi martani kan harin

Kwamishinan ƴan sandan jihar ya yi Allah wadai da wannan mummunan harin inda ya yi kira ga jama'a da su kwantar da hankulansu su ci gaba da ba jami'an tsaro haɗin kai.

Kwamishinan ya kuma tabbatar da cewa an fara gudanar da bincike domin cafko waɗanda ke da hannu wajen kawo mummunan harin.

ASP Maureen Chioma Chinaka, yayin da take magana a madadin kwamishinan ƴan sandan, ta bayyana cewa duk mai wani bayani komai ƙanƙantarsa ya ba jami'an tsaro domin zai taimaka wajen cafko masu hannu a harin.

Kara karanta wannan

'Yan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari a Arewacin Najeriya, Sun Sace Bayin Allah Da Kona Motocin Jami'an Tsaro

'Yan Bindiga Sun Halaka Sojoji a Zamfara

A wani labarin kuma, jami'an sojoji bakwai sun riga mu gidan gaskiya a wani farmaki da ƴan bindiga suka kai musu a jihar Zamfara.

Ƴam bindigan sun yi wa jami'an sojojin kwanton ɓauna ne lokacin da su ke kan hanyar zuwa kai agajin gaggawa domin daƙile harin ƴan bindiga.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng