Boko Haram: An Tsaurara Tsaro a Gidan Atiku Abubakar Na Jihar Adamawa
- An ƙara girke jami'an tsaro a gidan tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da ke Dougirei a Yola
- Wannan ya biyo bayam cafke yan Boko Haram da ke kulle-kulle kaddamar da hari a gidan ɗan takarar PDP a zaben 2023
- Mazauna yankin sun ci gaba da harkokinsu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ko tsoro ba
Adamawa state - An tsaurara matakan tsaro a gidan tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da ke Anguwar Dougirei a Yola babban birnin jihar Adamawa.
Wannan ya biyo bayan cafke wasu mutane da ake zargin mayaƙan ƙungiyar ta'addanci, Boko Haram ne da ke yunkurin kai hari gidan Alhaji Atiku.
Daily Trust ta rahoto cewa a ranar Lahadin da ta gabata ne ‘yan sanda suka kama wasu mutane hudu da ake zargin ‘yan Boko Haram ne da ke kulle-ƙullen kai hari gidan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP.
Wane hali mutanen Anguwar ke ciki bayan samun labari?
Yayin da wakilin jaridar ya ziyarci Anguwar ranar Talata, ya tarad da mutane cikin natsuwa suna harkokinsu na yau da kullum ba bu alamun tsoro a tattare da su.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Duk da barazanar kai hari gidan Atiku da ake zargin Boko Haram da shiryawa, mutanen da ke rayuwa a Anguwar sun buɗe shagunansu a lungu da saƙo suna harkokinsu.
Wani mazaunin Anguwar Dougirei a Yola, Sani Umar, ya ce matarsa ta shiga tashin hankali bayan samun lamarin cafke mayaƙan Boko Haram da ke shirin kawo hari.
Sai dai a cewarsa wani maƙocinsu ya kwantar mata da hankali da cewa Boko Haram ta mutu kuma ba zata iya kai hari Maiduguri ba ballantana Yola, Guardian ta rahoto.
Ya ce mazauna yankin ba su ji karar harbe-harbe ba ko kuma wani abu da zai iya haifar da firgici a yankin, yana mai cewa bayan sa'o'i da dama ne labarin lamarin ya fasu.
Dagaske yan ta'addan Boko Haram aka kama a Anguwar Atiku?
Wata majiya mai karfi ta jami’an tsaro ta shaida cewa wanda ake zargin da aka kama a gidan ya yi irin halin da ‘yan Boko Haram din suka saba yi.
Majiyar ta ce "Ya kasance mai karfin hali, mara tsoro da taurin kai yayin tambayoyi."
Wani mazaunin Yola a yankin gidan Atiku ya shaida wa wakilin Legit.ng Hausa cewa bai ga wani canjin a jami'an tsaron da ke gadin gidan tsohon mataimakin shugaban ƙasan ba.
Ya ce da yawan mutanen anguwar sun ɗauka labarin jita-jita ce kawai, kowa ya ci gaba da harkokin gabansa ba tare da fargabar wani abu ba.
Mutumin ya faɗa wa wakilin mu cewa:
"A gaskiya banga wani sauyi a masu gadin gidan Atiku ba, mu mun ɗauka labarin jita-jita ne, daga baya muka gane daga wurin 'yan sanda ya fito, ba wani abun damuwa, Allah ke tsarewa."
Yan Daba Sun Banka Wa Ofishin Kamfen Dan Takarar Gwamna a Jihar Kogi
A wani rahoton kuma Yan bindiga da ake zaton yan daban siyasa ne sun ƙona ofishin kamfen jam'iyyar SDP da ke Lokoja, jihar Kogi.
Ɗan takarar mataimakin gwamnan SDP a zaben gwamnan jihar da za a yi ranar 11 ga Nuwamba, Dakta Sam Ranti Abenemi ya bayyana yadda lamarin ya auku.
Asali: Legit.ng